Da Dumi-Dumi: Biden Yafadi Dalilin Da yasa Bai Bawa Isra'ila Bama-Bamai Ba Don Yaƙin Rafah

Dalilin Da Ya Sa Biden Ya Ƙi Bai Wa Isra'ila Manyan Bamabamai Don Yaƙi A Rafah.

Yanzu haka dai an kwashe kimanin watanni bakwai kenan Isra'ila na yaƙi a Gaza kuma ana ci gaba da samun rasa rayuka. To sai dai a yanzu kuma shugaban ƙasar Amurka, Joe Biden a wata tattaunawa da gidan talbijin na CNN, ya yi bayani kan dalilin da ya sa ya dakatar da aikewa da wasu manyan makamai mafi ƙarfi da Amurka ke da su zuwa Isra'ila.


Makaman sun haɗa da bamabamai masu ƙarfi nau'in 2000lb. Abin tambaya shi ne mene ne illar da bamabaman za su yi idan aka jefo su daga sama? A matsayinsa na makamin yaƙi, bam ɗin nau'in 2000lb yana da mummunar illar da zai haddasa. Majalisar Dinkin Duniya ta ce bam ɗin yana da ɓuraguzan da ke kisa daga nisan mita 350, sannan ɓaraguzan za su iya fasa ginin kankare mai kaurin mita uku sannan ya samar da rami mai girman mita 15.


Hakan ne ya sa ake ganin rashin dacewar yin amfani da shi a wurin da ke da dandazon farar hula kamar birnin Rafah. Ko da mutanen da ke da nisa da wurin da aka saka wannan bam to abin zai iya shafar su ta mummunar hanya. Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce "ƙarfin bam ɗin ka iya lalata huhu da jijiyoyin majina sannan kuma zai fatattaka gaɓɓai ɗaruruwan mitoci daga wurin da aka saka bam ɗin."


A bayyane take cewa duk da irin alƙawuran da Isra'ilar ta yi wa babbar ƙawartata wato Amurka cewa za ta kula wajen amfani da irin waɗannan makamai amma Amurkar ba ta aminta ba. Shugaba Joe Biden ba ya son Amurka ta zama tana da hannu wajen aiwatar da irin waɗannan hare-hare na sama da Isra'ila ke son yi a birnin Rafah da ke kudancin Gaza, inda aka yi ƙiyasin cewa akwai dandazon Falasɗinawa kimanin miliyan ɗaya da 400,000


Zanga-zangar ɗaliban Amurka kan yaƙin Gaza ta yi kama da lokacin Yaƙin Vietnam na 1968

9 Mayu 2024. Netzah Yehuda: Bataliyar Isra'ila da Amurka ke neman saka wa takunkumi kan yaƙin Gaza. Ministan harkokin cikin gida na Isra'ila mai ra’ayin riƙau ya yi allawadai da matakin da shugaba Biden ya ɗauka na ƙin samar da makaman Amurka da za a iya amfani da su a gagarumin farmakin da Isra'ila za ta kai kan birnin Rafah. Itamar Ben Gvir ya wallafa saƙo a shafinsa na X da ke cewa Hamas na ƙaunar Biden amma Shugaban kasar Isra'ila, Isaac Herzog, ya bayyana kalaman ministan a matsayin masu nuna rashin dattaku.


Da yake jawabi yayin bikin tunawa da nasarar da aka samu a kan Jamus a yaƙin duniya na biyu, Mista Herzog ya gode wa shugaba Biden da Amurka kan goyon bayan da ƙasarsa ke samu. Wakiliya ta ce rahotanni daga kafofin yada labaran Isra’ila na nuni da cewa jami’an tsaron ƙasar sun nuna matuƙar damuwa kan shawarar da babbar ƙasa mai samar masu da makamai ta ɗauka domin hakan na iya kawo cikas a ɓangaren tsaron Isra’ila.

Post a Comment

Previous Post Next Post