Da Dumi-Dumi: Wata Jami'ar Nigeria Ta Yaye Dalibai 5,545.

Jami’ar MAU Ta Yaye Dalibai Dubu 5,545 A Yola

Gwamna Ahmadu UmaruFintiri na jihar Adamawa, ya bukaci daliban da suka kammala karatu a jami’ar koyarwa ta Modibbo Adama da ke Yola (MAU), da su tashi tsaye da yin aiki tukuru, wajen tunkarar kalubalen da Nijeriya ke fuskanta a halin yanzu da nan gaba.

 Fintiri wanda mataimakiyarsa Farfesa Kaletapwa Farauta ta wakilta, ya bayyana haka lokacin da yake jawabi a taron yaye daliban jami’ar karo na 28 ranar Asabar a Yola, ya ce jami’ar ta yi kokari na kyankyasa, da kuma yaye daliban da za su bayar da tallafin da kasa ke bukata.


Cutar Kyanda Ta Yi Ajalin Mutum 42 A Adamawa

Dan Majalisa Ya Kaddamar Da Ajujuwa 3 A Firamare A Adamawa,Ya ci gaba da cewa “dukkanmu mun taru ba kawai domin mu muku tafi kawai don kun samu nasara ba, amma sai don taya ku murna don samun kyakkyawar makoma mai dorewa,” in ji Fintiri. 

 Haka kuma gwamna Ahmadu Fintiri, ya taya mataimakin shugaban jami’ar Farfesa Abdullahi Liman, murnar kammala shekaru biyar na shugabancin jami’ar, ya kuma taya mataimakin shugaban jami’ar murnar shirya taron yaye dalibai sau uku a cikin shekaru biyar.


Da yake jawabin bude taron tunda farko shugaban jami’ar Sarkin Akwa Ibom Mai Martaba Okuku Uwa Umoh Adiaka na 3 kuma mai rike da sarautar karamar hukumar Obot Akara, ya taya daliban da aka yayen murna da nasarar da suka samu.


Labarai Masu Nasaba

Gwamnatin Tinubu Ta Ba ‘Yan Jarida Cikakken ‘Yanci – Minista

An Yi Bikin Cikar Sarkin Lafiyan Bare-bari Shekaru 5 A Kan Karagar Mulki A Nasarawa Haka shima mataimakin shugaban jami’ar Farfesa Abdullahi Liman Tukur, ya amince da cewa ya cimma nasarorin ciyar da ci gaba da manufa da manufofin jami’ar ne da goyon baya, ya ce da ba zai samu ba idan bai samu hadin Kai da goyon baya ba.


Dalibai jimla dubu 5,545, suka kammala karatu a shekarar karatun ta 2022/3 a jami’ar, da suka hada da masu difloma 458, da 4,282 a fannin Digiri na farko, da zangon farko 53, zango na biyu 1,143 na sama, 2,376 a matakin kasa na biyu, zango uku 682 da digiri 28. A bangaren digiri na farko, an kuma ba da takardar shaidar kammala digiri ga dalibai 41, masu digiri na biyu 630 da kuma Ph.D 134 a fannoni daban-daban.

Post a Comment

أحدث أقدم