Wata Sabuwa: Ƙasar kenya Ta Kori Wani Dan Nigeria


Ƙasar Kenya Ta Kori Ɗan Najeriyar Da Aka Gani A Cikin Wani Bidiyio Yana Dukan Abokinyar Zamansa Da Ke Zaune A Kan Keken Guragu.


A ranar Asabar 4 ga watan Mayu ne aka fitar da ɗan Najeriyar, mai suna Nwankwo Noko daga Kenya, bayan ya daki budurwar tasa mai suna Pauline. Kyamarar tsaro ta CCTV ce ta ɗauki hoton Noko a lokacin da yake tsaka da bugun matar 'yan asalin Kenya da ke amfani da keken guragu. Da alama lamarin ya faru ne gidansu, A cikin bidiyon an ga mutumin na dukan abokiyar zaman tasa kafin wasu mata biyu su kawo mata ɗauki.



Ranar 29 ga watan Afrilu ne bidiyon ya karaɗe shafukan sada zumunta, lamarin da ya sa zaɓaɓɓiyar sanatar yankin Gloria Orwoba ta shiga cikin batun.'Yar majalisar ta gana da matar ranar 1 ga watan Mayu, sannan kuma aka kai ƙorafi zuwa ofishin 'yan sanda na Karen.



''Mutane ba sa iya kai ƙorafin cin zarafin da ake yi musu, ciki har da Pauline wadda ta shafe tsawon shekara 10 tana fuskantar cin zarafi'', in ji Owoba. Pauline na da 'ya'ya uku tare da mutumin. Sannan kuma ta ce Noko ya yi mata barazana ita da sauran ma'aikatan gidanta uku Idan Suka kuskura suka ce za su bayar da shaidar abin da ya farun a gaban kotu.

Post a Comment

أحدث أقدم