Da Dumi-Dumi: 'Yan Wasan Bayer Munich Sunce,"Dakatar Da Wasan Da Rafali Yayi yaudarane".

Dakatar Da Wasa Da Lafari Ya Yi Kafin Mu Farke Ƙwallo Yaudara Ce Kawai.

Kocin Bayern Munich Thomas Tuchel ya ce dakatar da wasa da alƙalin wasa ya yi kafin tawagarsa ta farke ƙwallon da Real Madrid ta zira musu "kamar yaudara ce". Bayern ce ke kan gaba da 0-1 bayan dawowa daga hutun rabin lokaci a wasan gab da ƙarshe na Champions League har zuwa minti na 88, lokacin da Joselu ya ci biyu cikin minti uku.

Bayan haka ne kuma a minti na 13 bayan cikar lokaci, Matthijs de Ligt ya farke ƙwallon amma kuma mataimakin lafari ya ɗaga tutar satar-gida. 'Yan wasan Real Madrid sun tsaya da wasan kafin De Light ya zira ƙwallon a raga, amma sai daga baya aka ga akwai yiwuwar babu satar-gidan kuma da na'urar VAR ta duba hukuncin. Saboda an tsayar da wasan, VAR ba za ta iya yin komai ba. 

Tuchel ya faɗa wa TNT Sports cewa "hukunci ne mummunan gaske" wanda kuma "ya saɓa wa dokoki". "Ana samu mummunan hukunci daga mataimakin lafari da kuma lafarin. Abin dai kamar wata yaudara ce daga ƙarshe," in ji shi." Mataimakin lafarin ya nemi afuwa amma hakan bai isa ba. Kawai ka ɗaga mana tuta a irin wannan lokacin.. "Lafarin ya ga lokacin da muka sake samun ƙwallon kuma muka buga ta raga. Abu ne mai wuya mutum ya yarda da hakan amma kuma abin da ya faru kenan. "Borussia Dortmund ce ta fara kaiwa wasan ƙarshen bayan ta doke PSG 4-2 gida da waje ranar Talata. Real za a buga wasan ƙarshen ne karo na 18 a Champions League ranar 1 ga watan Yuni a filin wasa na Wembley da ke birnin Landan.

Post a Comment

Previous Post Next Post