Hajjin Bana: Hukumar Aikin hajji Zata Taimaka Wa Alhazai.

Hajjin Bana: Alamomin Da Za Su Taimaka Wa Alhazai Cikin Harsuna 16 Ciki Har Da Hausa.

Hukumar Aikin Hajji da Umarah ta Kasar Saudiyya ta gabatar da wasu alamomi 15 da za su taimaka wa alhazai daga fadin duniya da za su gudanar da aikin hajjin bana a kasa mai tsarki. Wannan ci gaba na daga cikin tsare-tsaren da hukumar ta gabatar domin wayar da kan al’umma a yayin aikin hajjin bana na shekarar 1445 bayan hijira wanda ya yi daidai da 2024.

Labarai masu nasaba:

Hajjin Bana: Shettima Zai Kaddamar Da Jirgin Farko Na Maniyyata 430 A Kebbi

Matashi Ya Banka Wa Masallaci Wuta Yayin Da Ake Sallah A Kano

Hukumar ta sanar da hakan ne a shafukanta na kafofin sada zumunta da kuma shafinta na Intanet: https://guide.haj.gov.sa/

Hajjin Bana:

Alamomin za su taimaka wa alhazai wajen yin tambayoyi cikin harsuna 16 da suka hada da Larabci, Inglishi, Faransanci, Urdu, Bengali, Indonesian, Hausa, Amharix, Persian, Spanish, Turkish, Russina, Sinhalese, Uzbek da yaren Malaysia.

Labarai Masu Nasaba

Hajjin Bana: Shettima Zai Kaddamar Da Jirgin Farko Na Maniyyata 430 A Kebbi

Emefiele Ya Ki Amincewa Da Tuhumar Da Ake Masa A Kotu 

Alamomin za su taimaka wajen samar da bayanai da suka shafi lafiya, kwatance, harkar shari’a cikin tsarin taswira, kananan bidiyo da hotuna masu fadakarwa. Bugu da kari akwai tsarin da aka ware inda alhazai za su saurari sautin murya din yi musu bayani cikin sauki ta yadda za su fahimta.

Post a Comment

أحدث أقدم