Wata Sabuwa: An kama Wani Matashi Da Ya cinna Wa Masallaci Wuta

Yan Sanda Sun Kama Matashin Da Ya Cinna Wa Masallaci Wuta A Kano

Rundunar ‘yansandan Jihar Kano, ta kama wani matashi da ake zargi da cinna wa wani masallaci wuta, yayin da mutane ke tsaka da sallar Asuba. Lamarin da ya faru a garin Larabar Abasawa da ke Karamar Hukumar Gezawa a Jihar, ya jikkata mutane da dama.

An Dakatar Da Likita Saboda Sakaci A Jihar Kano

Matashi Ya Banka Wa Masallaci Wuta Yayin Da Ake Sallah A Kano Cikin wata sanarwar da kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, ta ce matashin mai suna Shafi’u Abubakar mai shekaru 38 ya shiga hannunsu bayan wani bincike da suka gudanar.

Hukumomin bayar da agaji a jihar sun mika akalla mutane 24 Asibitin Koyarwa na Murtala Muhammad da ke jihar, inda ake jinyar su. A gefe guda kuma wata majiya ta ce tuni mutum daya ya riga mu gidan gaskiya sakamakon munanan raunuka da ya samu sakamakon kunar wuta.

Labarai Masu Nasaba

Matashi Ya Banka Wa Masallaci Wuta Yayin Da Ake Sallah A Kano

Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar Da Harajin Tsaron Yanar Gizo

Shaida a garin sun bayyana cewar matashin ya yi amfani da man fetur wajen kunna wutar, bayan ya rufe masallata ta wajen masallacin. Kakakin ya ce binciken farko da suka gudanar a kan matashin, ya ce ya dauki matakin ne sakamakon gaza raba musu gadonsu da aka yi. A cewar matashin wadanda suka hana rabon gadon suna Masallacin a lokacin da ake sallar Asuba, wanda hakan ya sanya ya yanke hukuncin daukar matakin.

Post a Comment

أحدث أقدم