Puskas Arena Zai Karbi Ga Garumin Wasan Karshe A Champions League

Puskas Arena Zai Karbi Wasan Karshe A Champions League 2026

Za a buga wasan karshe a Champions League a 2026 a Budapest a filin da ake kira Puskas Arena, inji Uefa ranar Laraba, bayan tashi daga babban taron da ta gudanar a Dublin. Filin dake cin Æ´an kallo 67,215 shine wajen da tawagar Hungary ke buga wasanni, wanda ya karbi bakuncin wasa hudu a Euro 2020 da na karshe a Europa League tsakanin Sevilla da Roma.

An É—age taron zabar filin da zai shirya wasan karshe a 2027 zuwa watan Satumba, bayan da Uefa ke son jin karin bayani kan shirin gyaran San Siro, inda AC Milan da Inter ke wasanni. Haka kuma Uefa ta sanar da cewar za a buga wasan karshe a Champions League na mata a 2026 a Norway, Ullevaal Stadion. Shi kuwa filin wasa na Besiktas Park a Turkiya, zai shirya karawar karshe a Europa League a 2026 da kuma Europa Conference League a 2027.

Jamus za ta karbi bakuncin wasa biyu - Filin wasa na Frankfurk zai shirya wasan karshe a Europa League a 2027 da kuma Europa Conference League a 2026 a filin RB Leipzig da ake kira RB Arena. A wannan kakar ta 2023/24 za a buga wasan karshe a Champions League tsakanin Real Madrid da Borussia Dortmund a Wembley ranar 1 ga watan Mayu.

A karawar mata kuwa a bana za a kece raini tsakanin Barcelona da Lyon a San Mames, wato filin Bilbao a Sifaniya ranar Asabar 25 ga watan Mayu. An sake bayar da damar neman shirya wasan karshe a Champions League na mata na 2027, bayan da Uefa ta ce Stuttgart ba dama ta gudanar da wasan, sakamakon da aka bai wa Jamus bakuncin karawar da za a yi 2026 da kuma 2027.

Post a Comment

Previous Post Next Post