Da Dumi-Dumi: 'Yan Sanda sun Yi Nasarar Ceto Mutanen Da A kayi Garkuwa Dasu A Abuja

Yan sanda Sun Ceto Wadanda Aka Yi Garkuwa Da Su A Abuja

An Harbe Fitaccen Dan Bindigan Da Ya Addabi Mazauna Abuja A Sansaninsa Jami’an Rundunar ‘Yansanda ta birnin tarayya, Abuja, karkashin jagorancin kwamishina CP Benneth Igweh, sun ceto mutanen da aka yi garkuwa da su a unguwar Dawaki da ke Abuja ranar Lahadi. 

Kakakin rundunar ‘Yansandan birnin tarayya Abuja, SP Josephine Adeh, a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce, cikin gaggawa da dabaru na mayar da martani ga harin da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka kai a garin Dawaki a ranar 19 ga Mayun shekarar 2024, da misalin karfe 11:30 na dare, jami’an rundunar karkashin jagorancin Kwamishinan CP Igweh, da kansa sun yi gaggawar zuwa inda lamarin ya faru.

Yaushe Za A Dakatar Da Yi Wa `Yan Arewa Kisan Gilla? Mi’ara Koma Baya: CBN Ya Janye Dokar Cazar Kaso 0.05 A Banki

Cikin jarumtaka da hadin kai, ‘yansanda tare da hadin gwiwa da mafarauta, suka ci gaba da kai farmaki kan maharan, inda suka yi musu kwanton bauna a tsaunin Ushafa na Bwari da tsaunin Shiship na Mpape tare da musayar wuta wanda ya tilasta wa ‘yan bindigar tserewa da raunuka daban-daban inda ‘Yansandan suka yi nasarar ceto jama’ar.

Daya daga cikin wadanda aka ceto na kwance a asibiti ana kula da lafiyarsa inda kwamishinan ‘Yansandan ya jaddada jajircewar rundunar na tabbatar da zaman lafiya da tsaro a yankin, yayin da ake ci gaba da neman sauran wadanda aka yi garkuwa da su da suka tsere daga wurin yayin musayar wuta. Yan bindigar sun yi garkuwa da mutane 12 da suka hada da mata 8 da maza 4 a unguwar Frank Opara Street da ke Dawaki a Abuja.

Post a Comment

Previous Post Next Post