Da Dumi-Dumi: Haƙi Ƙanin Abun Da Ya Faru Agame Da Mutuwar Shugaban Kasar Iraƙ

An Gano Gawar Shugaban Kasar Iran, Ebrahim Raisi A Wajen Da Jirginsu Ya Yi Hatsari.

Shugaban na Iran Ebrahim Raisi ya samu rakiyar Ministan Harkokin Ƙasashen Waje Amira dollarIan, da gwamnan yankin Azebaijan ta Gabas a Iran da sauran jami’ai da masu kare lafiyar shugaban ƙasa. An gano gawar Shugaban Iran Ebrahim Raisi da ministan harkokin wajen ƙasar da sauran jami’ai a wajen da jirgi mai saukar ungulu ya yi hatsari, bayan an shafe sa’o’i ana nemansu a wani yanki mai tsaunuka da rashin kyawun hanya a arewa maso yammacin ƙasar, a cewar kafar watsa labaran gwamnati.

Gidan talbijin na ƙasar bai bayar da bayanai kan dalilin hatsarin jirgin ba a yankin Azebaijan ta Gabas a Iran. Sauran waɗanda suke cikin jirgin sun haɗa da Ayatollah Mohammad Ali Al-e Hashem - limamin masallacin Juma'a na birnin Tabriz da Janar Malek Rahmati watau gwamnan lardin gabashin Azebaijan. Kwamandan askarawan kare lafiyar shugaban ƙasa, Sardar Seyed Mehdi Mousavi, da waɗansu jami'an tsaron na cikin waɗanda suka yi hatsari a jirgin

Kawo yanzu ba a san musabbabin haɗarin jirgin sama mai saukar ungulun ba amma ɓangaren sufurun jirgin saman Iran ya fuskanci koma baya sakamakon takunkuman da Amurka ta sanya kasar. Bayan bayyanar labarin rasuwar shugaban Iran, Ebrahim Raisi mataimakin shugaban na ɗaya, Mohammad Mokhbar zai gaji kujerar shugabancin ƙasar kafin gudanar da zaɓe. Mokhbar zai riƙe muƙamin ne na watanni biyu kamar yadda tsarin mulkin ƙasar ta Iran ya zayyana, kafin sake gudanar da zaɓen shugaban ƙasar a cikin kwanaki 50. Kundin tsarin mulkin Iran ya fayyace kai-tsaye game da matakin da za a ɗauka da zarar an tabbatar cewa shugaban ƙasa ba zai iya gudanar da ayyukansa yadda ya kamata ba saboda rashin lafiya, ko mutuwa, ko tsigewa.

Alhakin zai koma kan mataimakin shugaban ƙasa na ɗaya - a wannan karon ana maganar Mohammad Mokhtar - don ya ci gaba da jagorantar ƙasar tare da haɗin gwiwar shugabannin majalisa. Sai kuma ɓangaren shari'a da zai jagoranci zaɓen sabon shugaban ƙasa cikin kwana 50.  Amma za a yi hakan ne kawai bisa umarnin jagoran addini, wanda shi ne ke da iko sama da kowa a sha'anin mulkin Iran. Bayan tabbatar da rasuwarsa da gidan talabijin ɗin ƙasar ya yi, yanzu ƙasar za ta gudanar da zaɓen.

Post a Comment

Previous Post Next Post