Da Dumi-Dumi: Shalƙwatan Tsaro Ta karyata Rahoton Sace Mutum 500

Shalƙwatar Tsaro Ta Karyata Rahoton Sace Mutane 500 A Zamfara

Shalƙwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta yi watsi da rahotan da ke ikirarin an sace mutane 500 da aka yi a ƙaramar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara. Daraktan yaɗa labarai na rundunar Sojin Manjo Janar Edward Buba, ya bayyana hakan ne a yau Juma’a cikin wata sanarwa inda yake cewa a zahiri an sace mutane huɗu ne kawai, saɓanin alƙalumman da ake yaɗawa.

Wani Sojan Amurka Ya Bankawa Kansa Wuta Don Nuna Goyon Bayansa Ga Falasdinawa. Sojoji Sun Fatattaki ‘Yan Ta’adda A Hanyar Tafiyarsu Ta Kai Hari Ga Al’ummar Jihar Kaduna Janar Buba ya jaddada cewa dakarun Operation Hadarin Daji suna aiki ne a cikin wani yanayi mai cike da ƙalubale, inda ya zama dole su magance haƙiƙanin gaskiya da kuma bayanan ɓata gari, musamman daga shafukan sada zumunta. Ya ƙara da cewa, maganar mutane 500 da aka yi garkuwa da su, wani ƙarin gishiri ne, inda aka tabbatar da sace mutane huɗu kawai.

Buba ya kuma ba da tabbacin cewa sojojin za su ci gaba da mai da hankali wajen fatattakar ƴan ta’adda, inda tuni aka kawar da shugabannin ƴan ta’adda da dama. Haka zalika ya ce; sojoji na haɗa kai da jami’an tsaro da al’ummar jihar Zamfara domin inganta tsaro. Duk da ƙalubalen da ake fuskanta.

Labarai Masu Nasaba

Tinubu Ya Kaddamar Da Gangami Yakin Neman Ilimi

Hajjin Bana: Hawa Da Gangarar Da Maniyyatan Nijeriya Suka Sha Kafin Fara Tash. Janar Buba ya kuma bayyana cewa sojoji na da ƙarfin faɗa da ƴaan ta’adda, inda suke samun nasarori a ayyukansu.

Post a Comment

Previous Post Next Post