Wata Sabuwa: Gwamnatin Jihar Sokoto Ta Yi Watsi Da Shirin Sauke Sarkin Musulmai

Wata Sabuwa: Gwamnatin Jihar Sokoto Tayi Watsi Da Yin Kurin  Sauke Sarkin Musulmai.


Gwamnatin jihar Sokoto ta yi watsi da rade-radin da ke cewa tana shirin tsige Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar III.
A cikin wata sanarwa a ranar Talata, mai magana da yawun gwamnatin jihar, Abubakar Bawa, ya yi tir da kokarin kawo cikas ga kyakkyawar alakar da ke tsakanin gwamnatin jihar da Majalisar Sarkin Musulmi.

Wannan jita-jita dai ta samo asali ne daga zargin da ƙungiyar kare hakkin Musulmi (MURIC) ta yi da ke ikirarin cewa gwamnatin jihar na yunkurin tsige Sarkin Musulmi.

Bayan haka ne mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya jaddada a ranar Litinin cewa matsayin Sarkin Musulmi wata cibiya ce da ake mutuntawa da ya kamata a kiyaye kuma a kare.

Da yake jawabi a wajen taro kan rashin tsaro a Najeriya da aka gudanar a jihar Katsina, Shettima ya bayyana muhimmancin rawar da Sarkin Musulmi ke takawa, inda ya bukaci mataimakin gwamnan jihar Sokoto Idris Gobir da ya kiyaye wannan matsayi da masarautar ta sarkin musulmai.

Gwamnatin jihar Sokoto ta bayyana zargin da kungiyar MURIC ta yi a matsayin maras tushe, inda ta tabbatar wa al’ummar musulmi cewa babu wani shiri na tsige Sarkin Musulmi.

Post a Comment

Previous Post Next Post