Inalillahi wa Innna Ilaihi Raji'un! Miji Da Mata Sun Rasu A Lokacin Aikin Hajji

Mata Da Miji Ƴan Amurka Sun Mutu A Lokacin Aikin Hajji

Wasu ma'aurata ƴan Amurka da suka mutu a lokacin aikin Hajji a Saudiyya sun shafe sama da sa'o'i biyu suna tafiya a cikin zafi kafin su mutu sakamakon tsananin zafi kamar yadda 'yarsu ta shaida wa BBC.

Alhaji Alieu Dausy Wurie mai shekaru 71 da Haja Isatu Wurie mai shekaru 65 a yankin Bowie dake jihar Maryland na daga cikin kimanin mutum 1,300 da suka mutu a yayin gudanar da aikin hajjin bana a ƙasar Saudiyya.

Tsananin zafi na bana ya wuce maki digiri 50 na ma'aunar salshiyos a wasu lokuta. Saida Wurie ta shaida wa manema labarai cewa tawagar da iyayenta suke ciki na yawon bude ido ta kasa samar musu da kayayyakin da ta yi alkawari da suka hada da abinci da isasshen ruwa.

Ma’auratan ‘yan asalin ƙasar Saliyo sun bace ne a ranar Lahadi 16 ga watan Yuni, makonni biyu da isa ƙasar Saudiyya.        Bayan kwanaki sai aka sanar da ƴarsu da cewa sun rasu. 'Yar da ke cikin makoki ta shaida wa BBC cewa aikin Hajjin na da matukar muhimmanci ga iyayenta.

Ma'auratan sun yi tafiya zuwa Gabas ta Tsakiya tare da gungun kusan mahajjata 100 ta wani kamfanin yawon bude ido na Amurka da ke aiki daga Maryland.

Post a Comment

Previous Post Next Post