Yanzu-Yanzu: Shahararan kamfanin Nan "Apple" Ya Saɓa Doka A Manhajarsa -Tarayyar Turai.

Da Dumi-Dumi: Kamfanin Apple Ya Saɓa Doka A Manhajarsa - Tarayyar Turai.

Hukumomin Tarayyar Turai sun zargi kamfanin Apple da laifin keta sabbin dokokin da aka tsara don sarrafa manyan kamfanonin fasaha.

Hukumar ta ce manhajar Apple na murƙushe kasuwannin abokan hamayya, wanda ke zama karo na farko da ya sami kamfani da ke saɓa dokar Kasuwar Dijital (DMA).

Kamfanin na fuskantar yuwuwar tarar kusan kashi 10 cikin 100 na kuɗaɗen shigar sa na duniya idan ya gaza bin ka'idoji.

An bai wa kamfanin Apple ɗin damar yin nazari kan sakamakon binciken farko da aka samu, kuma zai iya kaucewa cin tarar idan ya dawo da wata shawara wacce ta gamsar da Tarayyar Turai.

Kamfanin yana cajin masu haɗa manhajoji kaso 30 akan manhajarsa.

Post a Comment

Previous Post Next Post