Wata Sabuwa: Za A Fara Biyan Musu Ajiyan Banki Heritage Kuɗinsu Cikin Sati Guda NDLC

Za mu fara biyan masu Ajiya A Bankin Heritage Kuɗinsu Cikin Mako Ɗaya - NDIC.

Hukumar kula da harkokin bankuna a Najeriya ta NDIC ta ce za ta fara biyan masu ajiyar kuɗi a Bankin Heritage kuɗaɗensu cikin kwana bakwai. Shugaban hukumar, Bello Hassan, ya faɗa a yau Laraba yayin taron manema labarai cewa doka ta ƙayyade kwana 30 a matsayin wa'adin da za su biya kwastomomi kuɗinsu.

A ranar Litinin ne Babban Bankin Najeriya CBN ya ba da sanarwar ƙwace lasisin bankin saboda abin da ya kira "gazawa wajen inganta harkokin kuɗinsa". "Binciken farko-farko ya nuna kuɗaɗen ajiyar mutane sun kai naira biliyan 650 yayin da bankin ya ba da bashin biliyan 700," in ji Bello.

Ya ƙara da cewa daga cikin mutum miliyan 2.3 da suka ajiye kuɗi a bankin, kashi 99 cikin 100 ne suka ajiye ƙasa da naira miliyan biyar, wanda shi ne mafi yawan adadin da NDIC ke ba da inshora a kai.

Post a Comment

Previous Post Next Post