Yanzu-Yanzu: An Kama Ministan Wasanni Na Africa Ta Kudu Bisa Wasu Dalilai.

An kama Ministan wasanni Da Zargin Cin Hanci A Afirka Ta Kudu

An kama Ministan Wasanni na Afirka ta Kudu, Zizi Kodwa, bisa zargin cinhanci da rashawa. Ana kyautata zaton zai fuskanci tuhuma a gaban kotu da ta shafi karɓar kuɗi kusan dala 85,000 don nuna tasirinsa wajen ba da kwangilar wasu ayyukan gwamnati. Wani rahoton hukuma ne ya ambaci sunansa bayan ya binciki zarge-zarge kan wasu kamfanoni da mutane game da yadda gwamnati ta mamaye wasu harkoki.

Sai dai Mista Kodwa ya musanta duka zarge-zargen.

Mintuna 55 da suka wuceAn ƙirƙiro fasahar da matasa za su ga yadda za su zama idan sun girma, Bayanan hoto,Mutum zai riƙa magana da mutum-mutumin da aka yi mai ƙwaƙwalwa kamar shi.

Masana a jami'ar kimiyya da fasaha ta Massachusetts (Massachusetts Institute of Technology ) da ke Amurka, sun ƙirƙiro wata fasaha da za ta bayar da dama ga masu amfani da ita su iya yin magana da ƙirƙirarran mutum mai kamanninsu ta komai da ke zaman kamarsu idan sun girma. Wanan fasaha da aka yi wa laƙabi da "Future You" an tsara ta ne domin ta taimaka wa matasa nazari a kan kansu da kuma burinsu domin bunƙasa tunani da hankalinsu.

Fasahar tana samar da lissafi ko tunani da zai kasance daidai da na mai amfani da ita, inda za ta zo da tunani kusan daidai da yadda shi wannan mutum zai yi idan ya kai shekara sittin a raye. A nazarin farko da aka yi, masu amfani da fasahar sun nuna cewa sun samu raguwar fargaba, da kuma samun karin kauna da so da alaƙanta kansu da rayuwarsu ta gaba bayan ƴar tattaunawa da ƙirƙirarran mutum-mutumin.

Post a Comment

Previous Post Next Post