Yanzu-Yanzu: Al'ummar Garin Neje Na Ƙoƙarin Zaƙulo Mutanen Da Kasa Ta Danne

Ana Ƙoƙarin Zaƙulo Mutane 30 Da Ƙasa Ta Rufta Da Su A Neja

Mutum 30 ne ƙasa ta danne bayan wani ramin haƙar ma'adanai ya rufta a jihar Neja da ke tsakiyar Najeriya. Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Neja ta tabbatar da cewa mutum ɗaya ya mutu yayin da aka ceto mutum shida waɗanda suka samu raunuka.

Lamarin ya faru ne a ƙauyen Galkogo da ke ƙaramar hukumar Shiroro, kuma ana ganin cewa mamakon ruwan sama da aka samu ne ya haifar da lamarin.

Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa a jihar ta Neja, Abdullahi Baba Arah ya tabbatar wa BBC a safiyar yau Laraba cewa ana wani yunƙuri na samar da iskar shaƙa ga mutanen da ke maƙale a ƙarƙashin ƙasa. Neja na ɗaya daga cikin jihohin Najeriya waɗanda ke ƙunshe da albarkatun ƙasa masu yawa, wadda kuma ke fama da matsalar tsaro.

A irin waɗannan yankuna akan samu wuraren haƙar ma'adanai da ke aiki ba bisa ƙa'ida ba kuma ba a ɗaukan matakan kariya da suka kamata. Mintuna 29 da suka wuceMun ɗauki aniyar rage talauci da kashi 10 duk shekara a Jigawa - Gwamna Namadi

Mun ɗauki aniyar rage talauci da kashi 10 duk shekara a Jigawa - Gwamna Namadi", Tsawon lokaci 7,58

Bayanan bidiyo,Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo, Yayin da yake cika shekara ɗaya a matsayin gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi ya ce ɗaya daga cikin manyan manufofin gwamnatinsa shi ne rage talauci da kimanin kashi 10 cikin 100 a duk shekara.

Post a Comment

Previous Post Next Post