Yanzu-Yanzu: An Rufe Asibitin Farar Hula Na Ƙarshe A Birnin Sudan

An Rufe Asibitin Farar Hula Na Ƙarshe A Birnin Sudan

Likitoci a daya daga cikin asibitocin ƙarshe da ke aiki a birnin El-Fasher na Sudan da aka yi wa ƙawanya sun ce an tilasta musu rufe asibitin sakamakon harin da aka kai. Asibitin, wanda ke samun tallafin Médecins Sans Frontières (MSF), shi ne kawai wurin da ya rage inda farar hula da suka jikkata za su iya samun magani da kulawa.

 Kwanaki dai rahotanni sun nuna cewa harsasai sun afkawa asibitin wanda ya yi sanadin jikkatar mutane da kuma asarar rayuka. Sai dai kuma shaidun gani da ido a yanzu sun bayyana cewa mayaƙa daga cikin dakarun RSFsun mamaye wurin da asibitin yake.  Aranar Asabar ne dakarun RSF suka isa asibitin, suka buɗe wuta kuma suka yi awon gaba da magunguna da kayan aikin jinya tare da sace motar ɗaukar marasa lafiya da kai wa ma’aikatan asibitin hari.

Shugaban MSF a Sudan, Maximilien Kowalski, ya shaida wa BBC Newsday cewa, "saboda hargitsin, tawagarsu ba ta iya tantance ko akwai wadanda suka mutu ko suka jikkata ba." Ya kuma ce "ainihin asibitin yana kusa da filin yaƙi, don haka zai ci gaba da kasancewa a rufe a yanzu."

MSF na tura ayyukanta zuwa wani asibiti da ke kusa da ya lalace, wanda ba shi da man fetur da wutar lantarki, da ruwa, wanda ya saka fararen hula da suka ji rauni rasa samun kulawar da suke buƙata.  Harin dai ya nuna rashin bin doka da oda a yakin basasar Sudan.  Ana kuma zargin sojojin Sudan da ke yaki da dakarun RSF a cikin shekara guda da cin zarafi.

Kungiyar ta RSF, da aka ruwaito cewa Hadaddiyar Daular Larabawa ce ke mara mata baya—ko da yake jami’ai sun musanta hakan—sun tilasta rufe asibitin inda ake jinyar fararen hula.

Tun lokacin da rikicin ya fara a watan Afrilun 2023, sama da mutane 15,000 ne aka kashe, kuma kusan miliyan tara suka rasa matsugunansu, lamarin da ya zama rikicin gudun hijira mafi girma a duniya.  Ƙoƙarin da aka yi a tattaunawar zaman lafiya ya ci tura, inda ake zargin ɓangarorin biyu da ƙeta haƙƙin bil adama.

Post a Comment

Previous Post Next Post