Inalillahi Wa Innna Ilaihi Raji'un! Wani Manin Yaci Yarasu A Makkah Dan Nigeria Daga Jihar Kebbi

Hajjin 2024: Wani Alhaji Dan Nijeriya Daga Jihar Kebbi Ya Rasu A Makkah

Hukumar jin dadin alhazai ta Jihar Kebbi ta sanar da rasuwar wani maniyyaci a garin Makkah na kasar Saudiyya. A sanarwar da Alhaji Ahmed Idris, babban sakataren yada labarai na Gwamnan Kebbi, ya bayyana sunan marigayin da Abubakar Abdullahi daga garin Gulma da ke karamar hukumar Argungu.

Wata Hajiyar Jihar Kebbi Ta Rasu A Makkah, Shugaban NAHCON Ya Yi Ta’aziyya, Hajjin Bana: Yau Litinin Ita Ce Ranar Ƙarshe Ta Jigilar Maniyyata Zuwa Ƙasar Saudiyya. Sanarwar ta ce maniyyacin ya rasu ne bayan gajeruwar rashin lafiya. Marigayi Abdullahi daga Jihar Kebbi shi ne maniyyaci na uku da ya rasu a kasa mai tsarki.

Sanarwar ta ruwaito Gwamna Nasir Idris ya bayyana damuwarsa kan rasuwar tare da addu’ar Allah ya bai wa marigayin hutu na dindindin, ya gafarta masa. Tuni aka yi jana’izar marigayin jana’izar marigayin kamar yadda addinin Musulunci ya tanada aa Masjid Al-Ihram (Ka’aba), ranar Juma’a.

Labarai Masu Nasaba

Yau Litinin Gwamnati Da Ƙungiyar Ƙwadago Za Su Cimma Matsaya Kan Mafi Ƙarancin Albashi

Hajjin Bana: Yau Litinin Ita Ce Ranar Ƙarshe Ta Jigilar Maniyyata Zuwa Ƙasar Saudiyya

Post a Comment

Previous Post Next Post