Wata Sabuwa: 'Ƴan Jaridun Kano Sun Da Katar Da Kawo Rahotanni Daga Gidan Gwamnatin Kano

Yan Jarida Sun Dakatar Da Kawo Rahotanni Daga Fadar Gwamnatin Kano.

Kungiyar ‘yan jaridu ta kasa reshen jihar Kano ta sanar da kauracewa kawo rahoto ko wasu labarai na ayyukan gwamnatin jihar Kano. Wannan na zuwa ne bayan zargin cin zarafi da rashin girmama aikin ‘yan jarida da gwamnatin jihar da jami’anta ke yi wa ‘yan jarida.

Gwamnatin Kano Ta Biyawa Ɗalibai 119,903 Kudin Jarrabawar NECO Da NBAIS

Yau Litinin Gwamnati Da Ƙungiyar Ƙwadago Za Su Cimma Matsaya Kan Mafi Ƙarancin Albashi Ƙungiyar ta kuma soki gwamnati da mayar da kwararrun ‘yan jarida gefe tare da fifita waɗanda ba su da ƙwarewa ko kuma ƙwazo a wajen aiki.

Sakamakon haka, ƙungiyar ta ke sanar da dakatar da kawo duk wani rahoto ko labarai kan abubuwan da suka faru na gwamnati ko halartar taron manema labarai, ko yin hira da jami’an gwamnatin jihar har sai an sami cikakkiyar fahimta da kuma tabbatar da ‘yancin ‘yan jarida da kare lafiyarsu kafin mu ci gaba da aiki kamar yadda yake a ƙunshe cikin sanarwar.

Shugaban kungiyar, Aminu Ahmed Garko, ya jaddada muhimmancin ‘yan jarida na tabbatar da dimokuradiyya tare da yin kira ga daukacin ‘yan uwa abokanan aiki da su goyi bayan wannan shirin da kuma tabbatar da ‘yancin ‘yan Jarida.

 

Post a Comment

Previous Post Next Post