Da Dumi-Dumi: Gwamnatin Jihar Jigawa Ta Fara Bai Wa Ma'aikata Bashin Kudin Noma.

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙaddamar Da Bai Wa Ma'aikata Bashin Kuɗin Noma.

Gwamnatin jihar Jigawa a raewacin Najeriya ta ƙaddamar da shirin tallafa wa ma'aikata a ɓangaren noma.

Shirin ya tanadi bai wa ma'aikatan gwamnati bashi ta yadda za su iya bayar da tasu gudunmawa wajen noma wasu zaɓaɓɓun amfanin gona.

Shirin bayar da bashin zai samar da tallafin kayan aikin gona da kuɗin aiki don noma amfanin gona kamar shinkafa, da riɗi, da gero, da kuma dawa, inda ake fatan ma’aikatan za su biya bashin bayan kammala girbi.

Hukumomin jihar sun ce sun ɓullo da shirin ne la’akari da halin matsi da kuma tsadar rayuwa, ta yadda hakan zai bai wa ma’aikata damar noma abin da za su ci da kuma samun kuɗi.

Shugaban Ma'aikata Muhammad Kandira Dagaceri, shi ne shugaban kwamitin da ke kula da shirin bayar da bashin kuma ya ce sun buɗe wani shafi a internet inda ma’aikaci zai yi rajista. "Yanzu mun fara da ma'ikata 8,432 a kashin farko," in ji shi. 

Post a Comment

أحدث أقدم