Posts

Showing posts from September, 2024

Da Ɗumi-Ɗumi: NNPC Ya Ƙara Farashin Man Fetur Zuwa 855 A Kowace Lita.

Image
NNPC Ya Ƙara Farashin Man Fetur Zuwa 855 Kan Kowace Lita. Wasu gidajen sayar da man fetur na kamfanin mai na ƙasa (NNPC) l, na sayar da man fetur a kan Naira ₦855 ga kowace lita a wasu sassan Legas. Wannan na cikin wani faifan bidiyo ya nuna a shafukan sada zumunta.  Matatar Dangote Ta Fara Shirin Sayar Da Mai A Faɗin Nijeriya Tinubu Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Hajiya Dada Yar’adua Bidiyon wanda wani mai saye ya nuna rashin jin daɗinsa ya yaɗa, ya nuna cewa farashin litar kan wane kan famfo a gidan mai da ke Ikoyi, a Legas ya kai Naira 855 kan kowace lita. Lamarin ya zo ne a daidai lokacin da ake ƙara nuna damuwa game da tsadar man fetur wanda kwanaki shida da suka gabata, inda rahotannin kafafen yada labarai suka nuna cewa farashin man na iya yin tashin gwauron zabi zuwa Naira 1,300 kan kowacce lita, saboda matsalar kuɗi da NNPC ke fuskanta. Kamfanin wanda shi ne kaɗai mai shigo da man fetur a Nijeriya, ya sha musanta batun biyan tallafi, inda ya ce kawai yana sanya ido ne game da ku...