Posts

Inalillahi! An kashe Majinyata Da Dama Daga Zirin Gaza😭😭😭

Image
An kwashe Majinyata Da Dama Daga Zirin Ga. Mazauna Gaza Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce an kwashe wasu FalasÉ—inawa da suka ji raunuka da kuma marasa lafiya daga Gaza zuwa HaÉ—aÉ—É—iyar Daular Larabawa don neman magani. Wannan ne yunÆ™uri mafi girma na aikin kwashe majinyata da aka yi tun bayan fara yaÆ™in sakamakon harin da Hamas ta kai a kudancin Isra'ila ranar 7 ga watan Oktoba.  Majiyoyi a Gaza sun rawaito cewa an kwashe majinyata 150 cikin bas-bas biyar, amma har yanzu WHO ba ta tabbatar da asalin marasa lafiyan ba. Hare-haren da Isra'ila ke kaiwa a Gaza sun gurgunta fannin kiwon lafiyar yankin. Kuma an rufe babbar hanyar da ake bi domin kwashe marasa lafiya ta kan iyakar Gaza da Masar a Rafah bayan da sojojin Isra'ila suka karÉ“e iko da mashigar a farkon watan Mayu. WHO ta ce kawo yanzu kimanin Æ´an Gaza 5,000 ne suka samu kulawa a asibitoci da ke wajen yankin, amma har yanzu wasu 10,000 na buÆ™atar barin Æ™asar domin neman lafiya.  Tun kafin É“arkewar yaÆ™in wasu mazauna Ga...

Yanzu-Yanzu: Kamfanin Sadarwa Na MTN Ya Rufe Ofisoshin Sa Dake Nigeria.

Image
Kamfanin Sadarwa Na MTN Ya Rufe Ofisoshinsa Da ke Faɗin Najeriya A Yau Talata. Matakin kamfanin ba ya rasa nasaba da yadda wasu abokanan hulɗarsa da aka rufewa layin waya suka yi cincirindo a ofisoshin kamfanin har ma wasu suka yi ƙoƙarin kutsa kai don neman a buɗe masu layukan nasu. MTN ya rufe layukan mutane saboda sun gaza haɗa lambarsu ta ɗan ƙasa da layinsu. MTN ya wallafa sanarwar rufe ofisoshin nasa a shafinsa na X inda ya ce "ku sani cewa ofisoshinmu a faɗin Najeriya za su kasance a rufe yau 30 ga watan Yulin 2024.

Da Dumi-Dumi: 'Ƴan Ta’adda 284 Sun MiÆ™a Wuya Ga Sojojin HaÉ—aka

Image
Ƴan Ta’adda 284 Sun MiÆ™a Wuya Ga Sojojin HaÉ—aka. Nasarar yaki da ta’addanci na ci gagaba da samuwa, domin a tsakanin 10 zuwa 17 ga Yuli, 2024, mayakan Boko Haram 284 tare da iyalansu sun mika wuya ga rundunar hadin Gwuiwa ta kasa da kasa (MNJTF) a Kamaru.  Laftanar Kanal Abubakar Abdullahi, Shugaban sashen Hulda da Jama’a, ya bayyana cewa dakarun sashi na 1 sun karbi mayaka biyar a Wulgo a ranar 11 ga Yuli, 2024. Bayanai na farko sun nuna cewa wadannan mayakan sun fito ne daga Tumbuma da Kutumgulla a karamar kukumar Marte ta Jihar Borno, Nijeriya. A wannan ranar, Malum Kori Bukar, mai shekaru 50 da ya tsere daga maboyar Jibilaram, ya mika wuya ga dakarun. Haka zalika, mayaka 19 sun mika wuya a Madaya, Arewa Maso Gabashin Kamaru, da wasu 11 a Wulgo.  A ranar 12 ga Yuli, mayaka 64, ciki har da manya shida, mata 20, da yara 38, sun mika wuya a Bonderi, Kamaru. An Tafka Gumurzu, Sojoji Sun Kashe Ƴan Boko Haram Da Yawa, Wasu Sun MiÆ™a Wuya Boko Haram Sun Sace Wani Alkali Da Matarsa ...

Rikicin Masarautar Kano: Gmamtin Abba Kabir Yusuf Ta Sauya Alkibila

Image
Rikicin Sarautar Kano: Yadda Gwamnatin Abba Ta Sauya Alkibla . A wani lamari na sauya sabon salo dangane da rikicin sarautar Kano, Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya sake maido da masarautu uku daga cikin hudu da ya rushe. A rana daya Majalisar Dokokin Kano ta gabatar da kudirin samar da dokar kirkirar masauratun masu daraja ta biyu, aka yi mata karatun da ya kamata, aka zartar da dokar, sannan aka kai wa gwamna kuma ya rattaba mata hannu da yammacin ranar Talata. Bayan gwamna ya rattaba wa dokar hannu, nan take kuma ya amince da nadin sabbin sarakuna masu daraja ta biyu da suka hada da masarautun Gaya, Rano da Karaye. Gwamnan ya nada Alhaji Muhammad Mahraz Karaye, a matsayin Sarkin Karaye, wanda kafin nadinsa shi ne Hakimin Rogo. Sai kuma Alhaji Muhammad Isa Umar, a matsayin Sarkin Rano, wanda kafin nadinsa shi ne Hakimin Bunkure, sannan kuma Alhaji Aliyu Ibrahim Abdulkadir Gaya, a matsayin Sarkin Gaya, wanda shi ne tsohon Sarkin Gaya. Wannan mataki na gwamnatin Jihar K...

Da Dumi-Dumi: JAMB Ta Amince Da Maki 140 Zuwa 100 Mafi Karancin Maki Domin Shiga Manyan Makrantu.

Image
. JAMB Ta Amince Da Maki 140 Da 100 Mafi Karancin Maki Na Shiga Manyan Makarantu. Labarai Masu Nasaba Tsadar Rayuwa: ‘Yan Majalisa Sun Rage Albashinsu Da Kashi 50 Cikin 100 Gwamnatin Kaduna Ta Nisanta Kanta Akan Bidiyon Dukan Dan Balki Kwamanda . Hukumar shirya jarabawar shiga jami’o’i ta kasa (JAMB) ta sanya maki 140 a matsayin mafi karancin maki na shekarar 2024 da za a iya shiga jami’o’in kasar nan. Shugaban hukumar, Farfesa Ishaq Oloyede ne ya bayyana hakan a yayin tattaunawa da masu ruwa da tsaki kan bayar da takardar shiga manyan makarantu a shekarar 2024. Malamin Tsangaya Ya Shiga Hannu Kan Zargin Luwadi Da ÆŠalibai A Jigawa Da ÆŠumi-É—umi: Gwamnatin Tarayya Da Ƙungiyoyin Ƙwadago Sun Amince A Kan N70,000 Mafi Ƙarancin Albashi Oloyede ya ce, an amince da 100 a matsayin mafi karancin maki a Kwalejin Kimiyya da Kwalejojin Ilimi. Farfesa Ishaq ya bayyana cewa, wadannan mafi karancin maki da aka bayyana, su ne mafi Æ™anÆ™antar maki, amma hakan ba yana nufin dole ne hukumomin manyan makara...

Da Dumi-Dumi: Gwamnatin Jihar Jigawa Ta Fara Bai Wa Ma'aikata Bashin Kudin Noma.

Image
Gwamnatin Jigawa Ta Ƙaddamar Da Bai Wa Ma'aikata Bashin KuÉ—in Noma. Gwamnatin jihar Jigawa a raewacin Najeriya ta Æ™addamar da shirin tallafa wa ma'aikata a É“angaren noma. Shirin ya tanadi bai wa ma'aikatan gwamnati bashi ta yadda za su iya bayar da tasu gudunmawa wajen noma wasu zaÉ“aɓɓun amfanin gona. Shirin bayar da bashin zai samar da tallafin kayan aikin gona da kuÉ—in aiki don noma amfanin gona kamar shinkafa, da riÉ—i, da gero, da kuma dawa, inda ake fatan ma’aikatan za su biya bashin bayan kammala girbi. Hukumomin jihar sun ce sun É“ullo da shirin ne la’akari da halin matsi da kuma tsadar rayuwa, ta yadda hakan zai bai wa ma’aikata damar noma abin da za su ci da kuma samun kuÉ—i. Shugaban Ma'aikata Muhammad Kandira Dagaceri, shi ne shugaban kwamitin da ke kula da shirin bayar da bashin kuma ya ce sun buÉ—e wani shafi a internet inda ma’aikaci zai yi rajista. "Yanzu mun fara da ma'ikata 8,432 a kashin farko," in ji shi. 

Fifikon Manzon Àllah SAW Da Halittu Darasi Daga suratur Najmi.

Image
Fifikon Manzon Àllah SAW Da Halittu Darasi Daga suratur Najmi  Assalamu alaikum warahmtullahi Ta’ala wa barkatuh. Masu karatu barkan mu da sake haduwa a wannan makon. Idan ba a manta ba a karatunmu nFifikon Manzon Allah SAW: Darasi Daga Suratun Najmi (2)a makon da ya gabata mun tsaya ne a kan ayoyin da Manzon Allah (SAW) ya gani a lokacin da ya yi Mi’iraji. Isara’i da Mi’irajin Manzon Allah (SAW) duka suna nuna mana girman darajarsa ne a wurin Allah Tabaraka wata’ala. A Mi’iraji, Manzon Allah (SAW) ya ga Rafrafu, ya ga Jibrilu, ya ga Al’arshi, ya ga Kursiyyu, ya ga Magaryar Tikewa, ya ga Mustawad Darafaini (wani irin waje ne da misali idan ka yi kudu sai ka fito yamma, idan ka yi sama sai ka fito kasa, abu ne da ya fi karfin hankali). Falalar Ziyarar Kabarin Annabi SAW (2) Falalar Ziyarar Kabarin Annabi S.A.W (1) To amma me ya sa aka ce Manzon Allah ya ga wani bangare ne daga cikin ayoyin Ubangijinsa? Domin kamar yadda ayar ta ce “lakad ra’a min…”, ita “min” tana nuna wani bangare ...