Inalillahi! An kashe Majinyata Da Dama Daga Zirin Gaza😭😭😭

An kwashe Majinyata Da Dama Daga Zirin Ga.

Mazauna Gaza Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce an kwashe wasu FalasÉ—inawa da suka ji raunuka da kuma marasa lafiya daga Gaza zuwa HaÉ—aÉ—É—iyar Daular Larabawa don neman magani.

Wannan ne yunÆ™uri mafi girma na aikin kwashe majinyata da aka yi tun bayan fara yaÆ™in sakamakon harin da Hamas ta kai a kudancin Isra'ila ranar 7 ga watan Oktoba. 

Majiyoyi a Gaza sun rawaito cewa an kwashe majinyata 150 cikin bas-bas biyar, amma har yanzu WHO ba ta tabbatar da asalin marasa lafiyan ba.

Hare-haren da Isra'ila ke kaiwa a Gaza sun gurgunta fannin kiwon lafiyar yankin. Kuma an rufe babbar hanyar da ake bi domin kwashe marasa lafiya ta kan iyakar Gaza da Masar a Rafah bayan da sojojin Isra'ila suka karɓe iko da mashigar a farkon watan Mayu.

WHO ta ce kawo yanzu kimanin Æ´an Gaza 5,000 ne suka samu kulawa a asibitoci da ke wajen yankin, amma har yanzu wasu 10,000 na buÆ™atar barin Æ™asar domin neman lafiya. 

Tun kafin ɓarkewar yaƙin wasu mazauna Gaza kan samu kulawa ne a wajen yankin saboda tsarin kiwon lafiyar Gaza ba shi da isassun kayan aikin tunkarar wasu manyan cutuka.

Post a Comment

Previous Post Next Post