Mummunan Gobaran Takori Dubban Mutane A California.

Gagarumar Gobara Ta kori Dubban Mutane A California.

Shaidu sun bayyana cewa gobarar ta ƙone gidaje ƙurmus a yankuna da dama yayin da take ƙara matsowa zuwa birnin.

Mutane sun riƙa ficewa daga motoci suna arcewa a guje domin tsira da rayukansu, wasu sun bayyana lamarin a matsayin tamkar a fim.

A cikin sa'o'i kaɗan, iska mai ƙarfin gaske ta ruruta wutar dajin zuwa yankuna da dama na jihar California.

Aƙalla mutum 30,000 ne aka bai wa umurnin ficewa daga yankin yayin da gobarar ke bunƙasa, daga fili mai girman eka 10 zuwa 3,000.

Ɗaya daga cikin mazauna yankin ya ce ƴan kwana-kwana sun riƙa umartar mutane su fice daga motocinsu domin tsira daga wutar.

Jerin gwanon motoci suna tserewa daga yankin a baya can kuma hayaƙi ya turnuƙe.

Comments

Popular posts from this blog

Yanzu-Yanzu: Babbar kotun koli Ta Kasa Nigeria Ta Umarci Jam'iyyar PDP Ta Bai wa Tsohon Gwamnan Jigawa Daman Fitowa Takarar Shugabanci Jam'iyyar.

Abun-Mamaki: Wajen Jana'izar Sheik Dahiru Usman Bauchi /Sababbin kabarai na hausa EagleNewsHausa

Ana Wata Ga Wata: 'Yan Bindiga Sunyi Garkuwa Da Mata 12.