Yanzu-Ynazu: Falasdiwa Kusan Miliyan Daya Ne Suka Koma

Falasɗinawa Akalla  Dari Biyar  miliyan ne Zasu Koma Gida A Yau Talata.

Ana sa ran cewa Falasɗinawa sama da rabin miliyan za su koma gidajensu a arewacin Gaza a yau Talata.

Ƙungiyar Hamas ta ce sama da Falasɗinawa dubu 300 waɗanda yaƙi ya tarwatsa sun koma gidajensu da aka yi raga-raga da su a arewacin Gaza a ranar Litinin.

Hotunan da aka gani a yau sun nuna yadda Falasɗinawan ke tafiya a cikin motoci suna ratsa yankunan da aka yi wa rugu-rugu, sannan har yanzu akwai waɗanda suke taka sayyada a ƙoƙarinsu na komawa gida.

Ƙungiyar Islamic Jihad ta saki bidiyon da ke nuna cewa ɗaya daga cikin waɗanda za a saki, Abel Yehud, na nan a raye, wadda ake taƙaddama kan sakin ta tsakanin ɓangarorin biyu.

Isra’ila ta ce ta tabbatar cewa takwas daga cikin waɗanda aka tsara cewa Hamas za ta saki ƙarƙashin yarjejeinyar tsagaita wuta, sun mutu.

Comments

Popular posts from this blog

Yanzu-Yanzu: Babbar kotun koli Ta Kasa Nigeria Ta Umarci Jam'iyyar PDP Ta Bai wa Tsohon Gwamnan Jigawa Daman Fitowa Takarar Shugabanci Jam'iyyar.

Abun-Mamaki: Wajen Jana'izar Sheik Dahiru Usman Bauchi /Sababbin kabarai na hausa EagleNewsHausa

Ana Wata Ga Wata: 'Yan Bindiga Sunyi Garkuwa Da Mata 12.