Turkashi: Anci Zarafin Shugabar Kasar Mexico Cikin Bainar Jama'a

Shugabar Mexico Zata kai Ƙarar Mutumin Da Ya Taɓa Mata ƙrji a Cikin Jama'a kotu

Shugabar ƙasar Mexico, Claudia Sheinbaum, ta ce za ta maka wani mutum kotu bayan ya taɓa mata ƙirji tare da yunƙurin sumbatarta a cikin dandazon jama'a lokacin da take jawabi ga magoya bayanta.


A bidiyon da aka ɗauka da wayar hannu a ranar Talata, an ga mutumin ya kusanto ta daga baya inda yayi ƙoƙarin sumbatarta a wuya tare da dafa jikinta.

Hukumar tsaro ta tabbatar da cewa an kama mutumin.

A wata hira da ‘yan jarida ranar Laraba, Sheinbaum ta ce idan har za a iya yin haka ga shugabar ƙasa a bainar jama’a, to menene zai faru da sauran mata a ƙasar?


Ta ce ta ɗauki wannan matakin kotu ne saboda irin wannan cin zarafin abu ne da mata da dama ke fuskanta a Mexico, kuma ita kanta ta taɓa fuskantarsa tun kafin ta zama shugaba.


Comments

Popular posts from this blog

Yanzu-Yanzu: Babbar kotun koli Ta Kasa Nigeria Ta Umarci Jam'iyyar PDP Ta Bai wa Tsohon Gwamnan Jigawa Daman Fitowa Takarar Shugabanci Jam'iyyar.

Abun-Mamaki: Wajen Jana'izar Sheik Dahiru Usman Bauchi /Sababbin kabarai na hausa EagleNewsHausa

Ana Wata Ga Wata: 'Yan Bindiga Sunyi Garkuwa Da Mata 12.