Posts

Yanzu-Yanzu: An Sama Fahimatar Juna Tsakanin Ƙungiyar Ƙwadago Da Sakataren Gwamnatin Tarayya

Image
Yanzu-Yanzu: An Rufe Ƙofa Tsakanin Ƙungiyar Ƙwadago Da Sakataren Gwamnatin Tarayya Biyan Albashin Da Ƙungiyar Ƙwadago Ke Nema Na Iya Durƙusar Da Nijeriya. Yanzu-Yanz: A Karo Na 8, Gwamnati Ta Sake Kiran Zaman Sulhu Da Kungiyar Kwadago  A wani gagarumin yunƙurin warware yajin aikin da aka tsunduma a fadin kasar, sakataren gwamnatin tarayya George Akume na yin wata ganawar sirri da shugabannin ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya NLC da kuma TUC. Yajin aikin wanda ya fara a yau 3 ga watan Yuni ya biyo bayan gazawar gwamnatin tarayya na kammala tattaunawa kan sabon mafi ƙarancin albashi da kuma sauya ƙarin kuɗin wutar lantarki da aka yi a baya-bayan nan. Shugabannin ƙungiyoyin kwadagon da suka haɗa da shugaban NLC, Joe Ajaero da shugaban TUC Festus Osifo, sun bayyana matukar bacin ransu kan yadda gwamnati ke tafiyar da lamarin, musamman rashin halartar gwamnonin jihohi da wakilan tarayya da ke da hurumin yin alkawurra. Sun yi nuni da yadda gwamnati ta ƙi biyan buƙatunsu da kuma rashin taka ra...

Da Dumi-Dumi: Yajin Aiki Ya Kawo Tsaiko Akan Sauraran Shari'ar Sarakunan Kano

Image
Yajin Aiki Ya Hana Sauraren Shari’ar Sarakunan Kano. Yajin aikin da ƙungiyoyin ƙwadago suka yi a faɗin ƙasar nan, ya kawo cikas ga shari’ar babbar kotun tarayya da ke Kano dangane da matakin dakatar da Malam Muhammadu Sanusi II a matsayin sarki. Yajin aikin ya kai ga rufe kotun, tare da dakatar da ayyukanta.  A ranar Alhamis ɗin da ta gabata ne mai shari’a Mohammed Liman na babbar kotun tarayya da ke Kano ya bayar da umarnin hana gwamnatin jihar Kano aiwatar da dokar rushe majalisar masarautar Kano. Yadda Sarki Sunusi Lamido Ya Yi Bikin Shiga Fadar Kano Tsakar Dare, Khalifan Sheikh Ibrahim Inyas Daga Ƙasar Sanigal Ya Goyi Bayan Sunusi Lamido Sunusi II Umarnin ya biyo bayan buƙatar da Sarkin Dawaki Babba na Masarautar Kano, Alhaji Aminu Babba Ɗan Agundi ya yi, inda alƙalin umarci dukkan ɓangarorin da su dakata da aiwatar da komai har sai an saurari buƙatar mai ƙarar ranar 3 ga watan Yuni, 2024.  Duk da yajin aikin da aka yi na rufe harabar kotun, wata majiya ta nuna cewa kotu...

Da Dumi-Dumi: Ƙasar Sin Taba Da Shawar Wari Da Dama, Yadda Za A Dau Matakai Masu Tsauri Akan Matsalar Tsaro.

Image
Kasar Sin Ta Ba Da Shawarwari 6 Game Da Matakan Tsaro Yayin Tattaunawar Shangri-La A yau Lahadi ne ministan tsaron kasar Sin Dong Jun, ya gabatar da muhimmin jawabi a gun taron tattaunawar Shangri-La karo na 21 da aka yi a kasar Singapore, inda ya mai da hankali kan ra’ayin kasar Sin dangane da tabbatar da tsaron duniya. Dong ya ce, a wannan gabar da duniya ke fuskantar sauye-sauye, yana da matukar muhimmanci a kafa wani sabon tsarin hadin gwiwar tsaron yanki, wanda zai tabbatar da daidaita damar tofa albarkacin baki ga kasashen duniya, da kaucewa fadace-fadacen kungiyanci, da samar da mu’amala ta gaske, da sada zumunci da gaskiya kuma cikin daidaito. Na’urar Chang’e-6 Ta Kasar Sin Ta Sauka A Gefen Wata Mai Nisa Don Tattara Samfura Wang Yi Ya Gana Da Bakin Kasashen Larabawa Da Suka Halarci Taron Ministoci Karo Na 10 Na Dandalin Hadin-kan Kasar Sin Da Kasashen Larabawa.  Bisa wannan dalili ne kasar Sin ta gabatar da shawarwari guda shida, wadanda suka hada da kiyaye halaltacciyar m...

Yanzu-Yanzu: Bayan Shekaru 13, Tsofaffin Ma'aikatan Zamfara Sun Samu ₦5B

Image
Yanzu-Yanzu: Bayan Shekaru 13, Tsofaffin Ma'aikatan Zamfara Sun Samu  ₦5B Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya biya sama da Naira biliyan 5 ga ma’aikatan gwamnatin da suka yi ritaya bayan shafe shekaru 13 ba tare da an biya su kuɗin sallama ba. An fara biyan ne tun a watan Fabrairu bayan gudanar da tsarin tantance waɗanda suka yi ritayar.  A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, jihar ta biya Naira biliyan biyar da miliyan ɗari uku da arba’in da bakwai da Naira dubu ɗari biyu da arba’in da uku da Naira ɗari biyu da goma (5,347,243,210.00) ga waɗanda suka yi ritaya daga jihar da kuma ƙananan hukumomi a rukunnai biyar. Shekara Ɗaya A Mulki: Gwamna Lawal Ya Ƙaddamar Da Manyan Ayyuka A Ƙananan Hukumomin Zamfara. Shekara Ɗaya A Mulki: Ayyukan Ci Gaban Da Muke Yi Na Samun Tagomashi A Zamfara – Gwamna Lawal Sanarwar ta bayyana cewa an biya kuɗin sallama daga aiki ga malaman ƙananan hukumomi da na firamare 2,209 da ma’aikatan ji...

Da Dumi-Dumi: Jerin 'Yan Wasan Real Madrid. Da Suka Ɗauki 6 Champions League.

Image
Nacho Da Modric da Kroos Da Carvajal kowa Ya Ɗauki Champions League 6(Shida) Nacho da Modric da Kroos da kuma Carvajal, kowanne ya lashe Champions League na shida a tarihi. Ƴan wasan sun bi sawun gwarzon Real Madrid da ya fara ɗaukar babban kofin zakarun Turai shida daga 1956 da 1957 da 1958 da 1959 da 1960 da kuma 1966.Ranar Asabar a Wembley Real Madrid ta lashe La Liga na 15 jimilla da ake kira La Decimoquinta a Landan, inda ƴan wasan hudu kowanne ya ɗauki na shida kamar yadda Paco Gento ke da wannan ƙwazon. Kenan ƴan wasa biyar ne a tarihi da kowanne ya ɗauki Champions League shida, kuma dukkansu daga Real Madrid, koda yake Kroos ya lashe daya a Bayern Munich. Modric da Nacho da Carvajal duk sun lashe Champions League shida-shida a Real Madrid, yayin da Kroos ya dauki biyar a kungiyar da ɗaya a Bayern Munchen a Wembley a 2013. A kakar 2013/14 Nacho da Modric da kuma Carvajal suka fara ɗaga babban kofin zakarun Turai a karon farko a Lisbon a Real Madrid. Lokacin da Kroos ya koma Real...

Yanzu-Yanzu: Mbappe Babban Dan Wasan PSG Ya Amince Da Yarjejeniyar Komawa Real Madrid

Image
Mbappe Ya Kammala Yarjejeniyar komawa Real Madrid Mbappe ya saka hannu kan ƙwantiragin komawa Real Madrid daga Paris St-Germain, idan yarjejeniyarsa ya kare ranar 30 ga watan Yuni. Tun cikin watan Fabrairu ɗan ƙwallon tawagar Faransa ya amince baka da baka da cewar zai koma Sifaniya, sannan cikin watan Mayu aka sanar da zai bar PSG a karshen kakar nan. Mbappe mai shekara 25 ya saka hannun kan ƙunshin yarjejeniyar da Real Madrid ta gabatar masa, wanda zai koma Sifaniya ranar 1 ga watan Yuli da za a buɗe kasuwar cinikayyar ƴan ƙwallo a La Liga. Ana sa ran Real Madrid za ta sanar da labarin kammala ƙulla ƙwantiragi da Mbappe a mako mai zuwa daga nan ta gabatar da shi gaban magoya baya a Bernabeu kafin fara Euro 2024. Mbappe ya lashe kofin duniya a 2018, kuma shi ne kan gaba a yawan cin ƙwallaye a PSG mai 256 a raga, tun bayan da ya koma ƙungiyar aro daga Monaco a 2017. Ya amince da yarjejeniyar da za ta kare a Real zuwa karshen 2029, zai ke karbar £12.8m a kowacce kaka da karin ladan £128...

Yanzu-Yanzu: Gwamnatin Kebbi Ta Maida Asabar A Matsayin Ranar Tsaftan Muhalli

Image
Gwamnatin Kebbi Ta Ayyana Asabar Ɗin Karshe Wata A Matsayin Ranar Tsaftar Muhalli . G wamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya bayyana Asabar din kowane jarshe wata a matsayin ranar tsaftar muhalli a jihar. Gwamnan, ya bayyana haka ne wajen kaddamar da shirin tsaftar muhalli ta kowace karshe wata a jihar. Masu Baje Kolin Kaya Kimanin 300 Za Su Halarci Bikin Kasuwancin Yammacin Afirka A Legas. Gwamnatin Tarayya, Bankin Duniya Da Cibiyar IITA Za Su Bunkasa Noma Ta Fasahar Zamani Gwamnan wanda mataimakinsa, Sanata Umar Abubakar Tafida ya wakilta, ya bayyana cewa gwamnatinsa ta yanke shawarar sake bullo da kuma karfafa shirin tsaftacce muhalli na wata ne saboda muhimmancinsa ga lafiyar jama’ar. “Tsaftar muhalli da ruwan sha na da matukar muhimmanci ga jin dadin jama’a don rage cututtukan iska da na ruwa,” in ji shi. Ya kara da cewa, “Gwamnatina za ta ci gaba da kula da harkokin kiwon lafiya a Jihar Kebbi, a koda yaushe domin tabbatar da cewa al’ummarmu sun kasance ‘yan jiha masu koshin lafiya k...