Da Dumi-Dumi: Yajin Aiki Ya Kawo Tsaiko Akan Sauraran Shari'ar Sarakunan Kano

Yajin Aiki Ya Hana Sauraren Shari’ar Sarakunan Kano.

Yajin aikin da ƙungiyoyin ƙwadago suka yi a faɗin ƙasar nan, ya kawo cikas ga shari’ar babbar kotun tarayya da ke Kano dangane da matakin dakatar da Malam Muhammadu Sanusi II a matsayin sarki. Yajin aikin ya kai ga rufe kotun, tare da dakatar da ayyukanta. 

A ranar Alhamis ɗin da ta gabata ne mai shari’a Mohammed Liman na babbar kotun tarayya da ke Kano ya bayar da umarnin hana gwamnatin jihar Kano aiwatar da dokar rushe majalisar masarautar Kano.

Yadda Sarki Sunusi Lamido Ya Yi Bikin Shiga Fadar Kano Tsakar Dare, Khalifan Sheikh Ibrahim Inyas Daga Ƙasar Sanigal Ya Goyi Bayan Sunusi Lamido Sunusi II

Umarnin ya biyo bayan buƙatar da Sarkin Dawaki Babba na Masarautar Kano, Alhaji Aminu Babba Ɗan Agundi ya yi, inda alƙalin umarci dukkan ɓangarorin da su dakata da aiwatar da komai har sai an saurari buƙatar mai ƙarar ranar 3 ga watan Yuni, 2024.

 Duk da yajin aikin da aka yi na rufe harabar kotun, wata majiya ta nuna cewa kotun ta shirya cigaba da shari’ar kusan da tsakar ranar Litinin.

Amma rahotanni sun tabbatar da cewa shari’ar ta yi ƙudirin cigaba ta hanayar intanet duk da yajin aikin wanda ya shafi ayyukan kotu na yau da kullum.

Labarai Masu Nasaba

Khalifan Sheikh Ibrahim Inyas Daga Ƙasar Sanigal Ya Goyi Bayan Sunusi Lamido Sunusi II. Wata Sabuwa: Kotu Ta Hana Aminu Ado Da Sauran Sarakuna 4 Kiran Kansu Sarakuna A Kano

Post a Comment

Previous Post Next Post