Posts

Da Dumi-Dumi: Gwamnati Zata Fara Biyan 'Ƴan Bautan Kasa(NYSC) 77'000

Image
' Za Mu Fara Biyan 'Ƴan NYSC Alawus Din 77,000 Daga Wata Febrairu'. Shugaban hukumar kula da matasa masu yiwa ƙasa hidima NYSC, Birgadier Janar Yushau Ahmed ya ce za a fara biyan matasan alawus din naira 77,000 daga watan Fabrairun 2025. Shugaban hukumar ya faɗi hakan ne a jihar Katsina a lokacin da yake yi wa sabbin matasan da aka ɗauka na rukunin 'C' jawabi, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito. Yushau ya tabbatar da cewa ƙarin alawus ɗin na cikin kasafin kuɗin ƙasar na shekarar 2025 kuma zai fara aiki ne da zarar an amince da kasafin kuɗin. "Wannan watan na Janairu ya riga ya ƙare, amma da zarar an amince da kasafin kuɗin a watan Fabrairu mai kamawa, za ku fara karɓar naira 77,000 a maimakon 33,000 da ake biya yanzu,'' in ji shi. Ya kuma tabbatar wa matasan cewa ba za a aika su yankunan da babu tsaro ba. A ranar 25 ga watan Satumban bara ne dai gwamnatin ƙasar ta sanar da yi wa ƴan bautar ƙasa ƙari a alawus ɗin su zuwa naira 77,000 da zai soma aiki d...

Inalillahi! Motar Mai Ta Fashe A Jihar Jigaw

Image
'Ƴan Sandan Jihar Jigawa Sun Tabbatar Da Fashewar Tankar Mai A Dutse. Rundunar ƴan sandan Najeriya reshen jihar Jigawa ta tabbatar da fashewar tankar mai a wani gidan mai da ke Dutse, babban birnin jihar a daren jiya Alhamis. A cikin wata sanarwa da ya fitar, kakakin rundunar SP Lawan Shiius Adam ya tabbatar da cewa ba a samu asarar rai ko jikkata ba a haɗarin. Ya ce tankar ta fashe ne da misalin ƙarfe 7 na dare a gidan man Shakkato da ke kan titin Kiyawa a Dutse a lokacin da tankar ke ƙoƙarin juye man cikin tankin ƙarƙashin ƙasa. Kakakin rundunar ƴan sandan ya ce bayan samun labarin afkuwar lamarin, tawagar ƴan sandan yankin tare da masu kashe gobara suka yi gaggawar isa wurin inda aka yi nasarar kashe gobarar. Fashewar tankar mai dai ba sabon abu bane a ƙasar baki ɗaya, inda ko a watan Janairun nan kaɗai an samu fashewar tankar mai aƙalla sau uku, wanda ya janyo asarar rayuka fiye da 80. Ko a bara ma wata tankar mai ta faɗi a jihar ta Jigawa abin da ya kai ga mutuwar mutane 181.

Turkashi: Gaskiyar Magana Akan Seaman Abbas Ya Saki Matarsa(Hussaina)

Image
Namiji Ba Dan Goyo Bane": Da Gaske Seaman Abbas Ya Saki Matarsa Hussaina? Seaman Abbas Haruna ya karyata rade-radin cewa ya saki matarsa Hussaina, yana mai cewa suna tare cikin soyayya da zaman lafiya.  Ya kuma tabbatar da cewa matarsa ta kwanta asibiti har tsawon kwanaki 10 amma yanzu ta warke kuma tana shirin komawa gida Abbas ya ce babu wata matsala tsakaninsa da Hussaina kan kudin tallafi, yana zargin wasu ne ke kokarin haddasa rudani a tsakaninsu. Gombe - Seaman Abbas Haruna, sojan ruwan Najeriya da aka sallama daga aiki ya yi magana kan rade-radin da ake yadawa cewa ya saki matarsa Hussaina.  A cikin wani bidiyonsa da ke yawo a kafofin sada zumunta, Seaman Abbas ya warware rudanin da aka samu game da zamantewarsa da Hussaina.

Yanzu-Ynazu: An Gano Akwatin Da Yake Daukar Bayanai Na Jirgin Saman Da Yayi Hatsarin

Image
An Gano Bakin Akwatin Da ke Nadar Bayanai Na Jirgin Saman Amurka Da Yayi Hatsari. An gano baƙin akwatin da ke naɗar bayanan abubuwan da suka faru a lokacin da jirgin fasinjan Amurka ya yi haɗari. Yanzu haka jami'ai sun dukufa domin gano abin da ya janyo jirgin ya yi taho mu-gama da wani jirgi mai saukar ungulu na sojojin Amurka a yayin da ya ke ƙokarin sauka. Baƙin akwatin zai taimaka wajen gano abin da ya faru a lokacin haɗarin da kuma sauƙaƙawa masu bincike aikinsu. An yi amanna mutum 67 da ke cikin jiragen biyu sun mutu.H iragen sun yi taho mu-gama ne yayin da suke dab da sauka a filin jirgin saman Reagan da ke Washington DC. Mahukunta a Amurka sun ce za a kammala tattara dukkan bayanan da suka dace a game da haɗarin jiragen a cikin kwanaki 30. Sai dai Shugaba Trump ya ɗora alhakin haɗarin kan rikon sakainar kashi da gwamnatin Biden da ta wuce ta yi a fannin sufua sa ya lalace.

Innalillahi! Wani Mahaifi Ya Kashe 'Yarsa Saboda TikTok.

Image
Mahaifi Ya kashe ƴarsa Saboda Bidiyon Da Take Yi A TikTok. Wani mahaifi da ya mayar da iyalinsa Pakistan daga Amurka ya tabbatar da kashe ƴarsa bayan ya hana ta bidiyo a TikTok, kamar yadda ƴansanda suka bayyana. An gurfanar da Anwar ul-Haq ne bisa zargin kashe kai bayan ya tabbatar da kashe ƴarsa ɗin mai suna Hira a kudu maso yammacin birnin Quetta a ranar. Da farko ya bayyana wa masu bincike cewa wasu ƴanbindiga ne suka kashe ta. Mahaifin, wanda yake da shaidar zama ɗan Amurka, ya ce ya gano bidiyoyin da ƴarsa ke saki ba su dace ba. Ƴansanda sun ce suna duba yiwuwar mayar da kisar a matsayin kisar wadda ta ɓata wa danginta suna da ake kira 'humanity killing', lamarin da ba sabon abu ne a Pakistan, musamman a kan mata. Ɗaruruwan mutane - musamman mata- ake kashewa duk shekara a irin wannan kisan a Pakistan, kamar yadda ƙungiyoyin kare haƙƙi ɗan'adam suka nuna. Yawanci ƴan'uwa ne suke kashe wadda suke ganin ta jawo wa danginsu abin kunya. A game da Hira Anwar, wadda tak...

Yanzu-Ynazu: Israela Ta Kashe Fasdinawa Goma(10)

Image
Ma'aikatar Lafiyar Hamas Tace Isra'ila Ta Kashe Falasɗinawa 10. Ma'aikatar lafiya a Falasɗinu ta ce hari ta sama da Isra'ila ta kai yamma da gaɓar kogin Jordan da ta mamaye ya hallaka aƙalla Falasɗinawa 10. An kai harin ne a yankunan Tunbas da Samaria da ke arewacin kogin Jordan. Wakilin BBC ya ce ƴan makonnin nan Isra'ila ta zafafa kai hare-haren soji a arewacin yamma da gaɓar Kogin Jordan musamman a Jenin, inda hukumomin Falasɗinu suka gwabza faɗa da Hamas da mayaƙan jihadi. Hotunan bidiyo da ake kyautata zaton a garin Tamoun ne, ya nuna yadda mutane suka cika maƙil gaban wasu gine-gine da ya lalace domin zaƙulo waɗanda suka tsira da rai.

DA Dumi-Dumi: NlC Zata Yi Zanga-Zanga Adawa Akan Karin Kudin Kira.

Image
NLC Zata Yi Zanga-Zanga Don Adawa Da ƙarin kuɗin kiran Waya.  Ƙungiyar ƙwadago ta NLC a Najeriya ta ce za ta gudanar da gagarumar zanga-zanga ranar Talata 4 ga watan Febrairun 2025, domin adawa da ƙarin kuɗin kiran waya da kashi 50 wanda Hukumar Sadarwa ta Najeriya NCC ta amince da shi. Wata sanarwa da ƙungiyar ta hannun shugabanta Joe Ajaero, ya ce sun ɗauki matakin ne a wani taron gaggawa da suka gudanar ranar Laraba. NLC ta ce zanga-zangar za ta zama gargaɗi ga hukumomi kan yunkurin kakabawa mutane ƙarin kuɗin kiran waya a ƙasa kuma da albashi mafi ƙanƙanta bai wuce naira 70,000 ba, ga kuma ƙarin farashin mai da na abinci da lantarki da kuma ƙaruwar hauhawarar farashi. Ƙungiyar ta buƙaci rassanta na jihohi da su fara shirya mambobinsu domin shiga zanga-zangar ta ƙasa baki-ɗaya, inda ya yi kira ga ƙungiyoyin fararen hula da su ma su fito. Ta kuma yi kira ga ma'aikata da kuma ɗaukacin ƴan Najeriya da su tsaya kai da fata wajen yin watsi da wannan tsari da kuma waɗanda ba su a...