Turkashi: Gaskiyar Magana Akan Seaman Abbas Ya Saki Matarsa(Hussaina)
Namiji Ba Dan Goyo Bane": Da Gaske Seaman Abbas Ya Saki Matarsa Hussaina?
Seaman Abbas Haruna ya karyata rade-radin cewa ya saki matarsa Hussaina, yana mai cewa suna tare cikin soyayya da zaman lafiya.
Ya kuma tabbatar da cewa matarsa ta kwanta asibiti har tsawon kwanaki 10 amma yanzu ta warke kuma tana shirin komawa gida Abbas ya ce babu wata matsala tsakaninsa da Hussaina kan kudin tallafi, yana zargin wasu ne ke kokarin haddasa rudani a tsakaninsu.
Gombe - Seaman Abbas Haruna, sojan ruwan Najeriya da aka sallama daga aiki ya yi magana kan rade-radin da ake yadawa cewa ya saki matarsa Hussaina.
A cikin wani bidiyonsa da ke yawo a kafofin sada zumunta, Seaman Abbas ya warware rudanin da aka samu game da zamantewarsa da Hussaina.

Comments
Post a Comment