Yanzu-Ynazu: An Gano Akwatin Da Yake Daukar Bayanai Na Jirgin Saman Da Yayi Hatsarin

An Gano Bakin Akwatin Da ke Nadar Bayanai Na Jirgin Saman Amurka Da Yayi Hatsari.

An gano baƙin akwatin da ke naɗar bayanan abubuwan da suka faru a lokacin da jirgin fasinjan Amurka ya yi haɗari.

Yanzu haka jami'ai sun dukufa domin gano abin da ya janyo jirgin ya yi taho mu-gama da wani jirgi mai saukar ungulu na sojojin Amurka a yayin da ya ke ƙokarin sauka.

Baƙin akwatin zai taimaka wajen gano abin da ya faru a lokacin haɗarin da kuma sauƙaƙawa masu bincike aikinsu.

An yi amanna mutum 67 da ke cikin jiragen biyu sun mutu.H iragen sun yi taho mu-gama ne yayin da suke dab da sauka a filin jirgin saman Reagan da ke Washington DC.

Mahukunta a Amurka sun ce za a kammala tattara dukkan bayanan da suka dace a game da haɗarin jiragen a cikin kwanaki 30.

Sai dai Shugaba Trump ya ɗora alhakin haɗarin kan rikon sakainar kashi da gwamnatin Biden da ta wuce ta yi a fannin sufua sa ya lalace.

Comments

Popular posts from this blog

Yanzu-Yanzu: Babbar kotun koli Ta Kasa Nigeria Ta Umarci Jam'iyyar PDP Ta Bai wa Tsohon Gwamnan Jigawa Daman Fitowa Takarar Shugabanci Jam'iyyar.

Abun-Mamaki: Wajen Jana'izar Sheik Dahiru Usman Bauchi /Sababbin kabarai na hausa EagleNewsHausa

Ana Wata Ga Wata: 'Yan Bindiga Sunyi Garkuwa Da Mata 12.