A Jamhuriyar Nijar An Fara Samun Rarrabuwar Kawuna Tsakanin Kungiyoyin Farar Hula Masu Goyon Bayan Sojojin Da Ke Mulkin Kasar

 A Jamhuriyar Nijar An Fara Samun Rarrabuwar Kawuna Tsakanin Kungiyoyin Farar Hula Masu Goyon Bayan Sojojin Da Ke Mulkin Kasar, Yayin Da Wasu Ke Goyon Bayan Kasashe Irin Su Rasha, Wasu Na Cewa Nijar Ba Ta Bukatar Sojojin Wata Kasa Ta Waje.



Kungiyar da ke kare fararen hula ta MNSP ta ce muddin bayanai suka tabbatar da cewa akwai sa-hannun wata kasa a kisan da aka yi wa sojojin Nijar din 23 tare da jikkata 17, shakka babu za ta gabatar da korafin gaban Majalisar Dinkin Duniya.


Amma kungiyar ta ce akwai bukatar gwamnatin sojin kasar ta karfafa alakar da ke tsakaninta da kasashe irin su Rasha da sauransu.


Kodayake kungiyoyi irin su M62 na ganin cewa babu bukatar dauko dakarun wata kasa domin aikin wanzar da zaman lafiya a Nijar, yayin da suke zargin wanzuwar irin wadannan dakarun shi ke rura wutar rikicin da ke faruwa a kasar.


Post a Comment

Previous Post Next Post