Majalisar Wakilai Ta Amince Da Ƙudirin Dokar Ƙarin Albashi Da Alawus-alawus Ga Alƙalai

A Ranar Laraba Ne Majalisar Wakilai Ta Amince Da Ƙudirin Dokar Neman Ƙarin Albashi Da Alawus-alawus Ga Alƙalan Najeriya.






Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Shugaban kasar, Bola Ahmed Tinubu ya miƙa wa Majalisar kudirin dokar domin tantancewa tare da amincewa da shi a ranar Talata.

Ƙudirin da aka amince da shi ya bayar da albashin jimlar naira miliyan 5.3 a kowane wata ga alƙalin alƙalai na Najeriya (CJN).

Ƙudirin ya kuma ce sauran alkalan Kotun Koli za su samu albashin naira 4.2 yayin da Shugaban Kotun ɗaukaka ƙara zai rika samun albashin naira miliyan 4.4 duk wata.

Haka kuma, alƙalan kotun ɗaukaka ƙara za su rika karɓar albashin naira miliyan 3.7 duk wata, yayin da ƙaramin alƙali zai karɓi albashin naira miliyan 3.5 duk wata.

A cewar ƙudirin, albashin na wata-wata ya kunshi cikakken albashinsu ne da duk wani alawus-alawus na yau da kullum da suka haɗa da samar da mai da kuma kula da ababen hawa da dai sauransu.

Post a Comment

Previous Post Next Post