ALBISHIRINKU! HUKUMAR "JAMB" TA FITAR DA SAKAMAKON Jarabawar Na 2024

DA DUMINSA: JAMB Ta Bayyana Sakamakon Jarabawar UTME Na Shekarar 2024.



Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire, ko JAMB ta bayyana sakamakon jarabawar gama gari ta shekarar 2024.


 A cikin garuruwa 118 da sama da wurare 700 a fadin kasar, sama da 'yan takara miliyan 1.94 ne suka yi rajista kuma suka yi jarabawar. An bayyana sakamakon jarabawar UTME ne a ranar Litinin a wani taron manema labarai da magatakardar JAMB Farfesa Ishaq Oloyede ya gudanar a hedkwatar hukumar da ke Bwari, Abuja.


 A baya dai hukumar ta bayyana cewa ta yanke shawarar dage fitar da sakamakon jarabawar UTME da ‘yan kwanaki domin ba wa kanta isasshen lokaci domin ta yi nazari sosai kan sakamakon tare da tabbatar da gaskiya da amincin.



Hakan ya baiwa hukumar damar tabbatar da cewa babu tambayoyi ko wuraren rudani dangane da sakamakon da aka samu, musamman dangane da abin da ya shafi kwakwaf.

Post a Comment

Previous Post Next Post