Inalillahi! 'Yan Bindiga Sun Kai Wani Mummunan Hari A Birinin Tarayya (Abuja).

Da Ɗumi-ɗumi: ‘Yan Bindiga Sun Kuma Kai farmaki a babbn brinin Tarayya Garin Abuja, Sun Yi nasarar tafiya da Mutum hudu (4)




 


‘Yan Bindiga Sun Sake Kai Farmaki Abuja Tare Da Sace Mutum 5.

Wasu ‘yan bindiga a ranar Litinin da daddare, sun kai farmaki kan al’ummar unguwar Bmuko a Dutse Baupma a karamar hukumar Bwari a babban birnin tarayya Abuja, inda suka yi garkuwa da wasu mutane hudu.

Wani mazaunin unguwar, Isah, ya ce an kai farmakin ne da misalin karfe 11:50 na dare a gidan wani Injiniya Patrick, wanda matarsa ​​da dan uwansa na cikin wadanda aka yi garkuwa da su.




Gwamnati Na Buƙatar Dala Biliyan 10 Don Farfaɗo Da Ɓangaren Wutar Lantarki

Mamu Ya Nemi A Dauke Shi A Hannun DSS Zuwa Gidan Gyara Hali Na Kuje.   

A cewarsa, masu garkuwa da mutanen, wadanda adadinsu ya kai 30, sun kai farmaki yankin Zone C, Road 5 na al’ummar yankin, inda suka yi ta harbe-harbe a sama kafin su kutsa kai gidan Injiniyan, inda suka yi awon gaba da biyu daga cikin iyalansa.



Daya daga cikin shugabannin al’umma a yankin da ya so a sakaya sunansa, ya ce, sun ji karar harbe-harbe na ‘yan mintuna kafin karfe 12 na dare, a lokacin ne daya daga cikin masu gida da ke zaune a yankin, ya aika wa masu zaman haya a gidansa sakon murya ta shafin sada zumunta cewa, an kai musu hari.

Post a Comment

Previous Post Next Post