AN WULAKANTA GAWARWAKIN WASUN MUTANE BIYU A WANI GARI

 Jama'ar Garin Rigasa Sun Wulakanta Gawar Wakin Mutane Biyu (2) Da Hana Birnesu.




Wani mummunan al'amari ya faru a garin Kaduna! wasu mutane da ba'a san ko su waye ba sun shiga maƙabartar layin bola dake unguwar rigasa da wata motar asibiti (ambulance Car), Inda suka yi yunƙurin birne wasu gawarwaki guda biyu ba tare da sanin hukumar maƙabartar ba.

 

Bayan jama'ar gari sun sami labari shi ne suka je suka yo waje da gawarwakin da ba'a san ko na su waye ba, da kuma dalilin da yasa aka kashesu ba, sannan suka cinnawa motar asibitin wuta kamar dai yanda Kuke gani a a hotunan dake Kasa.

 

Zuwa yanzu dai ba'a san dalilin da yasa akayi yunƙurin birne gawarwakin a sirrance ba, kuma ba a san ko gawarwakin su waye ba, A taƙaice dai jama'ar gari sun ɗauki doka a hanunsu,wanda wannan yunƙurin ɗaukar dokar ne yasa aka rasa wadanda suka zo da gawar wakin, domin sun bi ta cikin Hayaniya sun sulale sun gudu.

 




Post a Comment

Previous Post Next Post