Shugaban Wata Jami'a Ya Nemi A Riƙa Yiwa Malaman Jami'ar Gwajin Shan Kwaya

Shugaban Jam'iar Abubakar Tafawa Balewa Da Ke Jihar Bauchi, Farfesa Muhammad AbdulAziz Ya Nemi A Riƙa Yiwa Malaman Jami'a Gwajin Shan Kwaya Ba Iya Ɗalibai Ba Kawai.



Farfesa Muhammud Abdulaziz ya yi wannan batu ne lokacin da yake bayanin ban kwana ga majalisar jami'ar a ranar Juma'a.


Ya ce " Ina ganin idan har za a riƙa yi wa ɗalibai irin wannan gwaji na shan kwaya, ina ganin mune ahaƙƙu da a yiwa, mu ma'aikata muma a mana ba kawai mu riƙa cewa a yi wa dalibai ba kawai."


"Mu ma mu mika kanmu a yi mana wannan gwajin domin mu tsaftace jami'o'inmu. Halayen arziki na da muhimmanci a wurin mu baki ɗaya.


"Idan har za a umarci dalibai  da su je su yi wannan gwajin domin tabbatar da lafiyar kwa-kwal-warsu, ina ganin babu wani abun damuwa idan suma malaman an yi musu irin gwajin.

Ina ganin cewa wannan ce hanyar daya da za a tabbatar da komai a jami'o'i," in ji Farfesan.

Post a Comment

Previous Post Next Post