Zargin Aikata Ta’addanci: Tukur Mamu Ya Nemi A Dauke Shi Daga Hannun DSS Zuwa Gidan Yarin Kuje

 

A yayin zaman kotun, Tukur Mamu Ta Hannun Lauyansa, Abdul Muhammad, Yayi zargin CEWAR hukumar tsaro ta DSS ta sabawa umarnin da kotun ta bayar a ranar 19 ga watan Disambar 2023, na cewa a barshi ya rika ganin likitansa domin duba lafiyarsa.



WASHINGTON DC - Mutumin da ake zargi da zama dan koren ‘yan ta’adda, Tukur Mamu, wanda ke fuskantar tuhume-tuhumen ta’addanci a gaban kotu ya bukaci babbar kotun tarayya dake Abuja ta sauya wurin da ake tsare da shi daga hannun hukumar tsaro ta DSS.



Ya shigar da bukatar Mai Shari’a Inyang Ekwo ya sauya umarnin daya bayar na cigaba da tsare shi a hannun hukumar tsaro ta dss zuwa gidan yarin Kuje.

A cikin hujjar daya gabatarwa kotun ta hannun lauyansa abdul muhammad, Tukur Mamu yayi ikrarin cewar sau daya tak aka bari ya gana da likitansa wanda ya gabatarwa hukumar DSS bukatar gudanar da cikakkun gwaje-gwaje kiwon lafiya akansa.



Tukuru Mamu yayi zargin cewar, tun bayar da aka gabatarwa hukumar DSS da rahoton likitan aka hana shi ganinsa kuma gashi yana bukatar ayi masa aikin tiyata a kowane irin asibiti a kasar nan

Post a Comment

Previous Post Next Post