Da Dumi-Dumi: Karin sojojin Rasha Da Kayan Aiki Sun Isa Nijar.

 

Da Dumi-Dumi: Karin sojojin Rasha Da Kayan Aiki Sun Isa Nijar.

,Kafafen yaɗa labaran Nijar sun ce ƙarin jiragen dakon kaya ɗauke da kayan aikin soji sun isa Yamai babban birnin ƙasar. Rahotanni sun ce wannan yana cikin wasa sabuwar yarjejeniyar tsaro da aka cimma tsakanin Nijar da Moscow.


Kazalika jirgin ya kawo abinci ga rukunin farko na sojin Rasha da suka je kasar a watan jiya- wadanda ake kira 'yan sanda Afrika. Alaƙar da ke tsakanin Amurka da Faransa ta yi tsami ne tun bayan juyin mulkin da aka hambarar da gwamnatin farar hula a bara.


Amurka ta amince za ta fara janye dakarunta dubu daya daga sansaninsu da ke cikin Nijar, mafi yawansu suna arewacin kasar. Nijar da wasu ƙasashen yankin Sahel na fama da matsalar masu ikirarin jihadi na tsawon shekaru.

Comments

Popular posts from this blog

Yanzu-Yanzu: Babbar kotun koli Ta Kasa Nigeria Ta Umarci Jam'iyyar PDP Ta Bai wa Tsohon Gwamnan Jigawa Daman Fitowa Takarar Shugabanci Jam'iyyar.

Abun-Mamaki: Wajen Jana'izar Sheik Dahiru Usman Bauchi /Sababbin kabarai na hausa EagleNewsHausa

Ana Wata Ga Wata: 'Yan Bindiga Sunyi Garkuwa Da Mata 12.