Da Dumi-Dumi: Majalisar Kaduna Ta Tattaunawa Da Tsofofin Masu Fada Aji.


Bincike :Majalisar Kaduna Ta Tattauna Da Tsoffin Kwamishinoni Da Manyan Sakatarori A Gwamnatin El-Rufai 

Gwamnatin Tarayya Na Biyan Tallafin Man Fetur A Asirce – El-Rufai. Kwamitin wucin gadi na Majalisar Dokokin Jihar Kaduna da ke binciken yadda aka gudanar da harkokin kudi a karkashin gwamnatin Gwamna Nasir el-Rufai, ya gayyaci tsoffin kwamishinoni da manyan sakatarori da wasu shugabannin kananan hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki a gwamnatin da ta gabata.


Idan dai za a iya tunawa, majalisar ta kafa kwamitin ne domin ya binciki harkallar kudaden jihar, lamuni, kwangila da sauransu daga ranar 29 ga watan Mayun 2015 zuwa 29 ga watan Mayun 2023 a lokacin da El-Rufai yake gwamnan jihar.


Karancin Wuta: Nijeriya Za Ta Daina Sayar Wa Kasashen Ketare Wutar Lantarki 

Shettima Zai Je Amurka Don Halartar Taron Kasuwanci Tsakanin Amurka Da Afirka Na 2024


Shugaban kwamitin Hon. Henry Magaji Danjuma, wanda ya zanta da manema labarai bayan wata tattaunawa ta sirri da tsoffin hadiman El-Rufai a daren ranar Litinin, ya ce: “Mun ga ya zama dole mu tattauna da su domin cimma nasara da kuma bayar da sahihin rahoton kwamitinmu.

” Hon. Dan juma, wanda shi ne mataimakin kakakin majalisar, ya ce, an bai wa duk wadanda aka gayyata dama ta musamman. Tun da farko dai, kwamitin ya fara tattaunawa da tsoffin shugabannin majalisun jihar na 8 da 9, Hon. Aminu Shagali da Hon. Yusuf Zailani a makon da ya gabata.

Post a Comment

Previous Post Next Post