Inalillahi! Wata Mata Ta Kashe Mijinta A Benewu

Matar Aure Ta Kashe Mijinta Saboda Yawan Jima’i A Benuwe

Wata matar aure mai shekaru 29 mai suna Torkwase Kpile ta daba wa mijinta wuka har lahira, bayan gardama ta barke a tsakaninsu saboda yawan jima’i a kauyen Achusa da ke karamar hukumar Makurdi a jihar Benuwe.  Eagle 🦅 Ta samu labarin cewa ma’auratan da suka yi aure watanni biyu da suka wuce, sun samu sabani kan yawan jima’i kafin matar ta dauki wuka ta daba wa mijin nata a wuya.

‘Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane 49 A Zamfara.  anata Hanga Ya Kare Sukar Da Ake Yi Masa Kan Tallafin Tukwanen Yumɓu Da Likafani

An bayyana cewa ta daba wa mijin nata mai suna Igbah Kpile, wuka a sassa da dama na jikinsa wanda daga bisani rai ya yi halinsa. Ihun da mijin ya yi shi ya jawo hankalin makwabtansu, wadansa suka shiga gidan suka tarar da shi kwance cikin jini.  Tun da fari matar ta yi korafin cewar mijin nata yana yawan damunta da jima’i, wanda har ta kai da ta fara gajiya.


Labarai Masu Nasaba

An Yi Bikin Cikar Sarkin Lafiyan Bare-bari Shekaru 5 A Kan Karagar Mulki A Nasarawa. Waɗanda Suka Mutu Yayin Turmutsutsun Karɓar Sadaƙa Ya Ƙaru Zuwa 7 A Jihar Bauchi

 

Ko da yake an garzaya da shi wani asibiti da ke Makurdi, amma kafin a karasa ya rasu.    Tun bayan faruwar lamarin, matar ta tsere kuma ‘yansanda na nemanta ruwa a jallo.  Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto mun kasa jin ta bakin kakakin rundunar ’yansandan jihar, SP Catheren Anene, domin karin haske kan lamarin.

Post a Comment

Previous Post Next Post