Shugaban Bola Ahmed Tinubu, Yace "Babu Tattaunawa tsakaninmu Da Amuruka Da Faransa Kan Kafa SAN Sanin Soja".

 Shugaban Kasar Nigeria, Bola Ahmed Tinubu Yace, "Babu Tattaunawa Tsakaninmu Da Amurka Da Faransa Kan Kafa Sansanin Soja - Gwamnatin Najeriya".

Gwamnatin Najeriya ta musanta batun cewa tana duba yiwuwar bai wa ƙasashen Amurka da Faransa damar kafa sansanin soja a ƙasar. Wata sanarwa da Minista Yaɗa Labarai Mohammed Idris ya aike wa BBC ta ce wannan batu "ba shi da tushe" kuma "gwamnatin tarayya ƙarƙashin mulkin Bola Tinubu ba ta yin wata tattaunawa da kowace ƙasa game da hakan".




A ƙarshen makon da ya gabata ne wasu cibiyoyi da manyan mutane a arewacin Najeriya suka rubuta wa gwamnatin wasiƙa suna gargaɗin kada a bai wa ƙasashen damar kafa sansanin soji Najeriya, bayan korar su da aka yi daga wasu ƙasashen yankin Sahel. "Muna neman jama'a su yi watsi da wannan ƙaryar," a cewar sanarwar.

"Ba mu samu wata buƙata ko tattaunawa da wata ƙasa ba kan wannan batu game da kafa sansanin wata ƙasar waje a Najeriya. Da ma tuni Najeriya na ci gaba da amfana daga aikin haɗin gwiwa wajen daƙile matsalolin tsaro." Tuni ƙasashen Nijar, da Mali, da Burkina Faso, da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya suka fatattaki sojojin Faransa da na Amurka daga ƙasashensu kuma suka gayyaci na Rasha.


Post a Comment

Previous Post Next Post