Inalillahi! Dan Dazon Mutanen Dake hijira Aduniya Dan Gudun Tashin Hankali kullum Ƙarawa Suke.

Yawan Mutanen Da Ke Tsere Wa Tashin Hankali A Duniya Na Ƙaruwa.

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayar da rahoton cewa mutane miliyan 120 ne aka tilasta musu barin gidajensu saboda yaki da tashin hankali da kuma tsanantawa, wanda ke nuna adadin ya ƙaru a shakera 12 a jere.

Hukumar ta ce yawan mutanen da suka rasa matsugunansu a duniya yanzu ya yi daidai da ɗaukacin al'ummar ƙasar Japan..Sabbin rikice-rikice a Sudan da Gaza sun ƙara ta'azzara munin al'amarin wanda babban jami'in hukumar, Filippo Grandi ya kira "mummunan lamari mafi girma kan halin da duniya ke ciki".

Ya buƙaci gwamnatoci da su magance matsalolin da ke haifar da irin waɗannan tashe-tashen hankula a maimakon yin gaggawar gyara kamar rufe kan iyakoki, lamarin da ya ce ba zai magance matsalar ba. A maimakon haka, ya yi kira da a haɗa gwiwa a tsakanin ƙasashen duniya don nemo mafita mai dorewa.

Rahoton na shekara-shekara na hukumar ya nuna cewa a Sudan, rikicin da ake ci gaba da yi tun a watan Afrilun 2023 ya yi sanadiyar raba mutane sama da miliyan tara da muhallansu.

A Gaza, rikicin da ke tsakanin Isra'ila da Hamas ya raba kusan kashi 75 cikin 100 na al'ummar kasar da muhallansu, adadin da ya kai miliyan 1.7 tun daga watan Oktoba. Har yanzu dai Syria ce ke fuskantar matsalar gudun hijira mafi girma, inda kusan mutane miliyan 14 suka rasa matsugunansu tun bayan ɓarkewar rikicin a shekara ta 2011.

Wasu miliyoyi kuma sun rasa matsugunansu a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango da Myanmar saboda fadace-fadacen da aka yi a shekarar da ta gabata. Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta jaddada cewa, galibin ‘yan gudun hijirar na samun mafaka ne a kasashe makwabta da masu karamin karfi zuwa matsakaitan ƙasashe masu tasowa.

Tun daga shekara ta 2012, yawan mutanen da suka rasa matsugunansu a duniya ya kusan nunkawa sau uku kuma ana sa ran za su ci gaba da ƙaruwa ba tare da wani sauyi a fagen siyasar ƙasashen duniya ba, Grandi ya ƙara da cewa. Hukumar ta yi Allah wadai da ɓangarorin da ke rikici da juna da suka saɓa wa dokokin kasashen duniya da kuma tursasa wa mutane tserewa daga gidajensu

Post a Comment

Previous Post Next Post