Rikicin Sarakuna: Tube Sarakunan Arewa Ba Mafita Bane


Rikicin Tube Sarakuna Bala’i Ne Ga Arewa’

Wani Masanin Tarihin Masarautun Gargajiya da Diflomasiyya a Jihar Kaduna, Alhaji Usman Dalhatu ya bayyana cewa; cire sarakuna wata babbar masifa ce da ke fuskantar Arewacin Nijeriya, duk da cewa irin wannan rikici ba wani sabon abu ba ne, lamarin ne wanda ke da asali tun a lokacin Turawan mulkin mallaka.

Dalhatu, wanda marubucin tarihi ne; sannan kuma makusanci ga marigayi Sarkin Zazzau, Shehu Idris ya bayyana cewa; muddin gwamnoni suka ci gaba da yi wa masarautun gargajiya karen-tsaye, ko shakka babu sun dauko hanyar ruguza Arewacin Nijeriya, musamman ganin yadda sarakunan ke bayar da gudunmawa wajen samar da zaman lafiya da kuma hadin kan al’umma baki daya.

Marubucin Tarihin ya bayyana haka ne, a zantawarsa da wakilinmu a Kaduna; inda ya fara da shimfida kan tarihin rikicin sarakunan da kuma Turawan Mulkin Mallaka.

“Wannan rikici na masarautun gargajiya da gwamnoni, bala’i ne da ke shafar Arewa a halin yanzu, wanda Turawan Mulkin Mallaka suka haddasa shi.

“A wancan lokaci, ayyukan da duk sarakuna ke yi; su ne Turawa suka kwace daga hannunsu, suka mayar da sarakunan karkashin gwamnan lardi a halin yanzu.

 Wannan shegantaka da gangan Turawa suka yi ta, saboda sun samu sarakunanmu da abin da ake cewa, (Well Define System of Gobernment), muna da majalisun dokoki; muna da na zartarwa, muna kuma da na bangaren shari’a, wanda duk duniya da shi ake amfani a lokacin mulkin dimokuradiyya, in ji shi

Post a Comment

Previous Post Next Post