Da Dumi-Dumi: Gwamna Zulum Ya Hana Gini A Magudanar Ruwa.

Gwamna Zulum Ya Hana Gine-Gine A Magudanar Ruwa.

Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum ya bayyana takaicinsa a kan yadda mutane suke gina gidaje a magudanar ruwa a jihar. 

Zulum ya bayyana haka ne a ranar Alhamis bayan ya kai ziyarar duba ɓarnar da ambaliyar - wadda ta ɗaiɗaita jihar - ta yi ga hanyoyin mota da gadoji da asibitoci da sauransu.

A cewarsa, "Ɓarnar ta yi yawa. Mun ziyarci wurare da dama mun gani. Akwai ban takaici yadda mutane suke gina gidaje a magudanar ruwa. 

Ba don a tare masa hanya ba, da ruwan zai riƙa bin hanyarsa yana wucewa ne.

"Duk da gargaɗin da ake yi, amma har yanzu mutane suna cigaba da gini a magudanar ruwa, wanda irin waɗannan matsalolin ne suka jawo ambaliyar. 

Ba za mu watsar da kula da rayuwar mutanen Maiduguri ba saboda wasu ɗaiɗaikun mutane," in jij shi kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

A ƙarshe ya yi kira ga ma'aikatar aikace-aikace da jami'an tsaro su tabbatar babu wanda ya sake yin gini a magudanar ruwa a jihar

Post a Comment

Previous Post Next Post