Alhamdulillah! Falasdinawa Suna Ta Komawa Gaza

Komawar Falasɗinawa Gaza Babbar Nasara ce - Hamas.

Falasɗinawa na komawa gidajensu da ke arewacin Gaza. Hamas ta ce komawar Falasɗinawa zuwa arewacin Gaza babbar nasara ce ga masu yunkurin ɗaiɗaita ƴan yankin.

"Komawar waɗanda aka ɗaiɗaita babbar nasara ce ga al'ummar mu da kuma ya nuna kasawa ko shan kaye ga masu shirin ɗaiɗaita da kuma mamaye yankin," in ji ƙungiyar yayin da aka buɗe mashigar komawa a yau.

Takwarar Hamas, Islamic Jihad, ta kira hakan da "martani ga dukkan waɗanda suka yi shirin ɗaiɗaita al'ummar mu".

A ranar Lahadi da daddare a Isra'ila, Firaminista Netenyahu ya ce buɗe mashigar na zuwa ne bayan da Hamas ta sauka daga matsayinta kan sakin Arbel Yehud wadda ta kasance cikin ƴan ƙasar da aka yi garkuwa da su.

"Hamas ta yi amai ta lashe kuma za ta cigaba da sakin ƙarin waɗanda ta yi garkuwa da su a Alhamis ɗin nan, 30 ga watan Janairu," kamar ofishin Netanyahu ya bayyana a shafin X

Comments

Popular posts from this blog

Yanzu-Yanzu: Babbar kotun koli Ta Kasa Nigeria Ta Umarci Jam'iyyar PDP Ta Bai wa Tsohon Gwamnan Jigawa Daman Fitowa Takarar Shugabanci Jam'iyyar.

Abun-Mamaki: Wajen Jana'izar Sheik Dahiru Usman Bauchi /Sababbin kabarai na hausa EagleNewsHausa

Ana Wata Ga Wata: 'Yan Bindiga Sunyi Garkuwa Da Mata 12.