Alhamdulillah! An Samu Zaman Lafiya Sosai A Kasar Cahdi
Ƙura Ta Lafa A Chadi Bayan Kai Hari Fadar Shugaban Ƙasar.
Ƙura ta fara lafawa a N'Djamena, babban birnin ƙasar Chadi, bayan da jami'an tsaro suka daƙile wani hari a fadar gwanatin ƙasar cikin daren da ya gabata.
Kakakin gwamnatin ƙasar, Abderaman Koulamallah ya ce maharan na ɗauke da ƙananan makamai.
Mista Koulamallah ya ce sojojin ƙasar sun kashe mutum 18 daga cikin maharan tare da kama shida dada cikinsu, yayin da soja guda ya rasa ransa.
Abderaman Koulamallah ya ce babban mai shigar da ƙara na ƙasar zai bayar da cikakken bayani kan maharan, amma ya ce ba ya tunanin harin na ta'addanci ne kamar yadda aka yi hasashe tun da farko.
Tuni aka tsaurara matakan tsaro a harabar fadar gwamnatin ƙasar.

Comments
Post a Comment