Da Dumi-Dumi: Gwamnan Bauchi Ya Kori Kwamishinoni Biyar
Gwamna Bala Ya Fatattaki Kwamishinoni 5 A Gwamnatinsa, Ya Ba Daa Sunayen Sababbi 8.
Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya sallami wasu daga cikin kwamishinoninsa domin inganta shugabanci da tabbatar da nagartaccen aiki ga al'umma Sanarwa ta bayyana cewa an tsige kwamishinonin ne domin kawo sababbin dabaru da kuzari don magance kalubalen da ke gaban gwamnati tare da kyautata ayyuka.
An Kuma tura sunayen mutane takwas don tantancewa a matsayin sababbin kwamishinoni, yayin da gwamnan ya jaddada kudurin gwamnatinsa na inganta rayuwar al'ummar jihar.
Bauchi - Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya sanar da sauye-sauye a gwamnatinsa tare da tsige wasu kwamishinoni guda biyar. Gwamnan ya ce ya dauki wannan mataki ne domin inganta shugabanci a gwamnatinsa da tabbatar da nagartaccen aiki.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai taimaka wa gwamnan kan harkokin yada labarai, Mukhtar Gidado, ya fitar a shafin Facebook.

Comments
Post a Comment