Da Dumi-Dumi: Gwamnatin Najeriya Ta Ayyana Lakurawa A Matsayin 'Ƴan Ta'adda.

Gwamnatin Najeriya Ta Ayyana Lakurawa A Matsayin 'Ƴan Ta'adda.

Gwamnatin Najeriya ta haramta ayyuka tare da ayyana ƙungiyar Lakurawa a matsayin ta ƴanta'adda.

Lakurawa ƙungiya ce ta ƴanbindiga da sunanta ya yi amo a bara, duk da cewa mazauna yankunan Sokoto da Zamfara da Kebbi da suke maƙwabtaka da Nijar sun ce sun daɗe suna shigowa jefi-jefi.

A takardar ƙara da gwamnatin ta shigar a wata babbar kotun tarayya da ke Abuja a ranar Alhamis, ta zargi ƴan ƙungiyar da aikata ayyukan ta'addanci da sata da garkuwa da mutane da kai hare-hare kan jami'an tsaro da ma'aikatan gwamnati.

Ta kuma zargi ƴan ƙungiyar da gurɓata tunanin mutane, ta hanyar ba su shawarar yi gwamnati bore.

Ministan shari'ar Najeriya, Leteef Fagbeni ya ce ƴan ƙungiyar na barazana ga tsaron Najeriya, wanda hakan ya sa suka buƙaci kotu ta haramta ayyukanta, tare da ayyana ta a matsayin ta ƴanta'adda.

Da yake yanke hukunci, Mai shari'a James Omotosho, ya haramta ayyukan ƙungiyar sannan ya ayyana ta a matsayin ta ƴanta'adda.

Comments

Popular posts from this blog

Yanzu-Yanzu: Babbar kotun koli Ta Kasa Nigeria Ta Umarci Jam'iyyar PDP Ta Bai wa Tsohon Gwamnan Jigawa Daman Fitowa Takarar Shugabanci Jam'iyyar.

Abun-Mamaki: Wajen Jana'izar Sheik Dahiru Usman Bauchi /Sababbin kabarai na hausa EagleNewsHausa

Ana Wata Ga Wata: 'Yan Bindiga Sunyi Garkuwa Da Mata 12.