Da Dumi_Dumi: 'Yan Boko Haram Sun Kashe Sojoji Da Dama A Borno.

Iswap Ta kashe Sojojin Najeriya Shida A Jihar Borno, Inji Rahoton AFP

Mayaƙa masu alaƙa da ƙungiyar Islamic State sun kashe sojojin Najeriya shida yayin wani hari da suka kai kan sansaninsu da ke jihar Borno a arewacin Najeriya, a cewar rahoton kamfanin labarai na AFP.

AFP ya ambato jami'an sojin Najeriya biyu na cewa maharan na ƙungiyar Islamic State West Africa Province (Iswap) sun far wa sansanin da ke Sabon Gari a ƙaramar hukumar Damboa ranar Lahadi da tsakar dare.

Rahotonni sun ce sun cinna wa sansanin wuta tare da ababen hawan da ke cikinsa.

"An kashe mana sojoji shida a harin na Iswap da suka kai sansanin bayan zazzafar musayar wuta," kamar yadda ɗaya daga cikin jami'an ya faɗa wa AFP.

Ɗaya jami'in ya ce jirgin sojin sama da aka aika daga binrin Maiduguri, mai nisan kilomita 100, shi ne ya kori maharan.

"Hare-hare ta sama ya kashe 'yanbindigar da yawa, ya lalata motoci da makamansu," in ji majiyar ba tare da bayar da yawan adadi ba

Comments

Popular posts from this blog

Yanzu-Yanzu: Babbar kotun koli Ta Kasa Nigeria Ta Umarci Jam'iyyar PDP Ta Bai wa Tsohon Gwamnan Jigawa Daman Fitowa Takarar Shugabanci Jam'iyyar.

Abun-Mamaki: Wajen Jana'izar Sheik Dahiru Usman Bauchi /Sababbin kabarai na hausa EagleNewsHausa

Ana Wata Ga Wata: 'Yan Bindiga Sunyi Garkuwa Da Mata 12.